Karamar magana ta zama babba: Batun raba masarautar Kano gida 4 ta samu tagomashi

Karamar magana ta zama babba: Batun raba masarautar Kano gida 4 ta samu tagomashi

Batun kirkirar sabbin masarautu masu cin gashin kansu guda hudu daga masarautar Kano ta Sarki Muhammadu Sunusi II na cigaba da daukan hankalin jama’a musamman yadda a yau kudurin ya tsallake karatu na farko a majalisar.

Idan za’a tuna Legit.ng ta ruwaito wani mutumi mai suna Salisu Ibrahim ya aiko ma majalisar bukatar kirkirar sabbin masarautu guda hudu a jahar Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya, musamman duba da cewa dokar Soji ce ta samar da masarautar Kano.

KU KARANTA: Badakalar bindiga da kudi: Ganduje ya sake farfado da binciken Sarkin Kano

Karamar magana ta zama babba: Batun raba masarautar Kano gida 4 ta samu tagomashi

Majalisar dokokin Kano
Source: UGC

A zaman majalisar na ranar Talata, ta karbi rahoton kwamitinta mai kula da kananan hukumomi da nade naden shwagabannin gargajiya da kuma kwamitin shari’a na majalisar dangane da bukatar kara ma wasu masu rike da sarautun gargajiya zuwa matsayi na daya.

Illar wannan aiki da majalisar Kano ta dauka a shine hakan zai karya lagon mai martaba Sarkin Kano, hakan zai rage masa karfi da iko da kuma karsashi, amma a hannu guda matakin zai kara ma sabbin Sarakunan da za’a nada iko.

A wani labarin kuma hukumar yaki da rashawa da karbar koke koke ta jahar Kano ta sake farfado da binciken data fara yi akan mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II game da zargin da take yi masa na bindiga da kudaden asusun masarautar Kano.

Kimanin shekaru biyu da suka gabata ne dai hukumar ta fara kaddamar da wannan bincike, amma daga bisani ta dakatar dashi bayan majalisar dokokin jahar Kano ta dakatar da nata binciken a ranar 22 ga watan Mayun 2017, kamar yadda Ganduje ya bukata.

Wata wasika da hukumar ta aika ma sakataren masarautar ta umarci wasu manyan ma’aikatan fadan Sarki guda hudu su bayyana a gabanta don amsa tambayoyi game da kudaden da masarautar ta kashe daga shekarar 2013 zuwa 2017, jami’an sun hada da shugaban ma’aikatan mai martaba Sarki, Mannir Sunusi, sakataren Sarki, Mijitaba Abubakar, babban akantan fada, Mohammad Kwaru da tsohon sakataren sarkin, Isa Sunusi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel