Manyan kasashe mafi talauci (kalli matsayin Najeriya)

Manyan kasashe mafi talauci (kalli matsayin Najeriya)

Ana tantance karfin tattalin arzikin kasashe ne ta hanyar cigaban da suke samu ta hanyar kasuwanci, da kuma yawan jarin da kasar ta ke da shi, da kuma tasirin da tattalin arzikin ya ke da shi ga al'ummar da ke zaune a wadannan kasashe.

Hakan ne ya sanya ake amfani da tattalin arzikin kasashe wurin tantance kasar da ke da arziki da kuma wacce ta ke fama da talauci.

A binciken da masana a fannin tattalin arziki su ka yi, ya nu na cewa manyan kasashe guda 10 da suka fi ko ina fama da matsalar tattalin arziki suna yankin nahiyar Afirka, inda Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta ke a matsayin ta daya da ta fi kowacce kasa talauci a duniya, duk kuwa da cewa kasar ta na da albarkatun kasa masu yawan gaske.

Manyan kasashe mafi talauci (kalli matsayin Najeriya)

Manyan kasashe mafi talauci (kalli matsayin Najeriya)
Source: UGC

Kasa ta biyu da ta ke biye wa Congo, ita ce kasar Mozambique, kasashen Uganda da Tajikistan su ne suka zo a matsayin na uku dana hudu a jerin kasashen.

KU KARANTA KUMA: Najeriya na bukatar tsayayyen jagora kamar Shugaban kasa Buhari – Babban malami

5. Kasar Yemen ita ce ta ke a matsayin ta ta biyar. Sai dai kuma kasar ta Yemen ta na fama da yakin basasa.

6. Kasar Haiti ita ce ta ke a matsayin ta shida a jerin kasashen, kasar ta na fama da matsalar yanayi, inda har babban bankin duniya ya bayyana cewa kashi 90 na al'ummar kasar suna zaune ne cikin hadari.

7. Kasar Ethiopia ita ce kasa ta bakwai a jerin kasashen. Kasar ta na fama da matsalar talaucin ne saboda, makwabciyar ta kasar Djibouti, ta zama ita ce babbar tashar jiragen ruwa. Amma kuma duk da haka an bayyana kasar a yanzu a cikin jerin kasashen da tattalin arzikin su ya ke habaka sosai a yankin Afirka.

8. Kasar Tanzania ita ce ta fito a matsayin kasa ta takwas. Kasar ta na samun habakar tattalin arziki a yanzu, yayin da talauci ya samu koma baya a kasar in ji babban bankin duniya.

9. Kasa ta tara ita ce kasar Kyrgyzstan. Kasar ta samu matsalar tattalin arziki ne saboda dogaron da ta yi wurin shigo da zinare.

10. Kasar Uxbekistan ita ce kasa ta 10 a jerin kasashen, yayin da tattalin arzikin kasar ya ke ta habaka daga shekarar 2004 zuwa 2016.

Kasar Najeriya ita ce kasa ta 20 a cikin jerin kasashen.

Manyan kasashe mafi talauci (kalli matsayin Najeriya)

Manyan kasashe mafi talauci
Source: UGC

Manyan kasashe mafi talauci (kalli matsayin Najeriya)

Manyan kasashe mafi talauci
Source: UGC

Manyan kasashe mafi talauci (kalli matsayin Najeriya)

Manyan kasashe mafi talauci
Source: UGC

Idan ba ku manta ba majiyarmu Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa a wani rahoto da ta samu ya nu na cewa Najeriya da kasar Afirka ta kudu, sune suke da tattalin arziki mafi yawa a fadin nahiyar Afirka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel