Wata sabuwa: An dakatar da sana’ar Acaba a wasu manyan jahohin Arewa guda 5

Wata sabuwa: An dakatar da sana’ar Acaba a wasu manyan jahohin Arewa guda 5

Hukumar rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta sanar da haramta duk wani aiki daya danganci sufurin baburan haya wanda aka fi sani da suna Acaba a wasu manyan jahohin Arewacin Najeriya wadanda matsalolin tsaro suka dabaibayesu.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan kasa, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu cikin wata sanarwa daya fitar, inda ya zayyano jahohin da dokar ta shafa kamar haka; Kano, Katsina, Kebbi, Zamfara, Sokoto, Kaduna, Kebbi da Neja.

KU KARANTA: Atiku ya haramta naira dubu goma goma da Buhari ke rabawa na Trader Moni

Wata sabuwa: An dakatar da sana’ar Acaba a wasu manyan jahohin Arewa guda 5

An dakatar da sana’ar Acaba a wasu manyan jahohin Arewa guda 5
Source: Depositphotos

Rundunar tace ta dauki wannan mataki ne domin hana ma yan bindiga walwala da damar zirga zirga, musamman duba da cewa basa amfani da motoci, da babura suke amfani wajen kaddamar da hare hare.

“Wannan ne dalilin da tasa rundunar ta dauki wannan mataki na haramta aikin Acaba a yankunan dake da kusanci ko makwabtaka da dazukan da Sojoji suke aiki inda yan bindiga suke amfani dasu a matsayin mafaka, mabuya ko sansanoninsu.

“Mun san wannan mataki zata shafi jama’a mazauna yankunan, amma akwai bukatar amfani da duk wata dama da zata yiwu wajen gurgunta ayyukan yan bindiga tare da kawo karshensu domin samar da dawwamammen zaman lafiya a Najeriya a yankin, don haka jama’a su bada hadin kai.” Inji shi.

Sanarwar ta jaddada cewa dokar ta shafi yankunan dake da kusanci ko suke makwabtaka ne da dazukan da yan bindiga suka yi katutu a jahohin Zamfara, Kebbi, Kano, Kaduna, Katsina, Sokoto da Neja ne kadai.

Daga karshe rundunar Sojan ta nemi hadin kan gwamnatocin jahohi dasu taimaka mata wajen sanar da jama’a game da wannan sabon doka, ta yadda jama’a zasu fahimci dokar, kuma zasu baiwa Sojojin hadin kan daya dace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel