Ba mu gano Basaraken da aka yi garkuwa da shi a Mahaifar Shugaban kasa ba – ‘Yan Sanda

Ba mu gano Basaraken da aka yi garkuwa da shi a Mahaifar Shugaban kasa ba – ‘Yan Sanda

Mun ji labari cewa Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya ya tura wata Runduna domin tayi kokarin ceto Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar, da wasu ‘yan bindiga su ka sace a makon da ya gabata.

Jaridar Punch ta rahoto cewa IGP, Mohammed Adamu, ya aika wasu kwararrun Jami’an ‘Yan Sanda na musamman da su ka hada har da Tawagar SARS zuwa jihar Katsina domin kawo karshen sace-sacen jama’a da ake faman yi.

Wannan Runduna da aka aika za tayi kokarin ganin ta kubuto da Surukin Dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Magajin Gari, Alhaji Musa Umaru da aka yi garkuwa da shi a Ramar Laraba da yamma a gidansa.

Mai magana da yawun bakin ‘Yan Sanda na yankin jihar Katsina, Gambo Isa ya bayyanawa menama labarai wannan a Ranar Juma’a 3 ga Watan Mayu. Isa yace amma har yanzu dai ba a dace wajen gano Alhaji Musa Umaru ba.

KU KARANTA: Boko Haram sun ci karfin Sojojin Najeriya a wani Kauyen Borno

Ba mu gano Basaraken da aka yi garkuwa da shi a Mahaifar Shugaban kasa ba – ‘Yan Sanda
Ana neman wanda su ka sace Surukin Dogarin Shugaban kasa
Asali: Twitter

Rundunar da aka aika zuwa Garin Daura da ke jihar Katsina sun hada da wasu Dakaru na shugaban ‘yan sanda, Rundunar SARS, da PMF da kuma jami’an da ke maganin ta’addanci. Amma duk da haka babu labarin wannan Basarake.

Jami’an tsaron sun nemi jama’a su taimaka masu da hadin kai da karin bayani domin maganin wannan ta’adi na masu garkuwa da mutane da kashe Bayin Allah. Yanzu dai an kara jami’an tsaro bayan sace Magajin Garin na Daura.

‘Yan Sanda sun baza ma’aikata ko ina a cikin Garin Daura domin maganin rashin tsaro a yankin. A gaban gidan Sarki dai akwai tarin motocin ‘yan sanda, sannan kuma jami’an tsaro na ta faman sintiri a ko ina cikin jihar Katsina.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel