Gazali Tanimu ya zama Gwarzo a Jami’ar Sarki Fahad ta Saudi-Arabiya

Gazali Tanimu ya zama Gwarzo a Jami’ar Sarki Fahad ta Saudi-Arabiya

- Matashi daga Arewacin Najeriya ya kafa tarihi a Kasar Saudiyya

- Gazali Tanimu ya kammala PhD yana da shekara 27 rak a Duniya

- Tanimu shi ne ya zama Gwarzo a cikin kaf ‘Daliban Jami’ar a bana

Mun samu labarin wani Bawan Allah mai suna Gazali Tanimu, wanda ya je har kasar Saudiyya ya nuna irin basirar da yake da ita. Yanzu dai sunan wannan Matashi ya ratsa ko ina bayan ya zama Gwarzon bana a jami’ar KFUPM.

Gazali Tanimu ya zama Zakaran shekarar karatun bana na 2018/2019 inda ya lashe kyautar ‘dalibin da ya fi kowa kokari a cikin sahun masu karatun Digiri na uku watau PhD. Yanzu dai wannan Matashi ya zama Dakta na ilmin Boko.

KU KARANTA: Jami'an Hisbah za su rika cafke gandaye a lokacin Azumi

Gazali Tanimu ya zama Gwarzo a Jami’ar Sarki Fahad ta Saudi-Arabiya

Gazali ya je har Jami’ar kasar Saudiyya ya ciri tuta
Source: Facebook

A kaf jami’ar King Fahad University of Petroleum and Minerals ta Saudi Arabia. Gazali Tanimu, shi ne ‘Dalibin PhD da ya fi kowa hazaka a wannan shekarar. Tanimu ya fito ne daga Garin Zaria da ke cikin Jihar Kaduna a Najeriya.

Malam Gazali Tanimu ba yau ya saba yin irin wannan fice ba, ko a lokacin da yake Digirinsa na biyu na Masters a wannan babbar jami’a ta kasar Saudi, ya gama ne da matakin farko, kuma ya zama ‘Dalibin da ya zo na daya a shekarar.

Tanimu, yayi Digirin farko ne a harkar Chemical Engineering a jami’ar Ahmadu Bello, inda a nan ma ya nunawa Duniya baiwarsa. Abin da zai burge ka game da wannan Saurayi shi ne, ya kammala karatun na sa ne yana shekara 27.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel