Shugaba Buhari ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a Jami'ar Tarayya da ke Dutse

Shugaba Buhari ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a Jami'ar Tarayya da ke Dutse

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da ayyukan tituna da magudannun ruwa da aka gina a kan kudi naira biliyan 1.4 a Jami'ar Gwamnatin Tarayyya da ke Dutse a Jihar Jigawa.

Shugaban kasar, wanda Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurahman Bello Danbazau ya wakilta ya ce ayyukan sun hada da titi mai tsawon kilomita 4.5 a cikin jami'ar da kuma magudanen ruwa fiye da kilomita biyu wanda ya fara daga cikin jami'ar zuwa wani kududufi da ke kusa da gonar jami'an.

Shugaban kasar ya sake jadada cewa babu wata bangare na kasar nan da za a bari a baya domin banbancin siyasa ko wata dalili.

Shugaba Buhari ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a Jami'ar Tarayya da ke Dutse
Shugaba Buhari ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a Jami'ar Tarayya da ke Dutse
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya yi korafi a kan yawan yajin aikin malaman jami'o'i

Ya ce ayyukan da aka gudanar na karkashin shirin asusun bayar da tallafi ne da gwamnatinsa da amince da shi tun cikin farkon shekarar 2018.

A jawabin ta, shugaban jami'ar, Farfesa Fatima Batul-Mukhtar ta ce samar da gine-gine yana da matukur muhimmanci ga cigaban makarantun gaba da sakandire, inda ta ce "Jami'ar Tarayya na Dutse ta kasance tana fama da matsalar tituna da magudanen ruwa tun kafa ta a shekarar 2011."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel