Garin Zariya ya cika makil wajen yaye ‘Daliban Jami’ar ABU

Garin Zariya ya cika makil wajen yaye ‘Daliban Jami’ar ABU

A jiya 27 ga Afrilu ne babbar jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Garin Zariya ta yaye dubunnan ‘Daliban ta da su ka kammala Digirin farko da na biyu watau Masters da kuma Digirin PhD, da Difloma a bangarori da dama.

Sarakuna da Attajirai da kuma masu mulki sun halarci wannan katafaren taro da shugaban jami’ar, Farfesa Ibrahim Garba ya shirya. Wannan ne karo na 41 a tarihi da jami’ar mai shekara kusan 57 da kafuwa da yaye ‘Daliban ta.

Garin Zariya ya cika makil wajen yaye ‘Daliban Jami’ar ABU

Gwamnan Kaduna, Dangote da Shugaban NUC a Jami’ar ABU
Source: Twitter

Jami'ar ta dai yaye 'dalibai sama da 15,000 a wannan shekarar, wanda aka samu 81 da su ka gama da ajin Digiri na matakin farko. An ba zakakarun cikin wadannan 'Dalibai kyauta ta musamman. Daga cikin manyan abubuwan da su ka faru shi ne:

KU KARANTA: Jama’a sun yi wa Dino Melaye dafifi a Jami’ar ABU Zaria

Garin Zariya ya cika makil wajen yaye ‘Daliban Jami’ar ABU

Mai kudin Afrika Aliko Dangote cikin alkyabbar ABU Zaria
Source: Instagram

1. Dangote ya samu shaidar Dakta

Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya zo wannan jami’a inda aka mika masa shaidar Dakta saboda irin gudumuwar da yake badawa. Dangote ya zo ne tare da ‘Diyarsa Halima Dangote har ya bude dakunan da ya bude.

2. Manyan kasa sun cika Zariya

Mai martaba Sarkin Zazzau da gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna yana cikin wadanda su ka karbi Masaukin baki a taron. Tsohon gwamnan Jigawa, shugaban hukumar NUC da kuma Femo Otedola sun halarci wannan biki.

3. Dino Melaye ya ci taro

A baya kun ji cewa Dino Melaye yana cikin ‘daliban da jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta yaye a wannan shekarar. ‘Dan majalisar ya kammala karatunsa na Digirgir ne a tsangayar harkokin siyasa da huldodin kasashen waje.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel