Wani ‘Dan Jarida zai bada filin da Ganduje ya ba sa domin ayi aikin Allah

Wani ‘Dan Jarida zai bada filin da Ganduje ya ba sa domin ayi aikin Allah

Mun samu labari cewa a kwanakin baya ne Mai girma Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada kyautar wani makeken fili ga wani Bawan Allah, amma shi kuma yace zai yi sadaka da shi.

Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta yankawa Nasiru Salisu Zango fili daga cikin fegin da ke Unguwar Bandirowa a cikin kwaryar birnin Kano. Nasiru Salisu Zango wanda ‘dan jarida ne, yayi watsi da wannan kyauta ta gwamna.

Wannan ‘dan jarida da ake aiki a gidan Freedom Radio, ya bayyana wannan ne a shafin sa na sadarwa na zamani na Facebook. Zango ya fito yace idan akwai wadanda ke da bukatar wannan fili domin yin wani aikin Allah, su zo su karba.

KU KARANTA: Ganduje ya bada umarni a ba Ma'aikatan INEC filaye ana shirin zabe

Wani ‘Dan Jarida zai bada filin da Ganduje ya ba sa domin ayi aikin Allah
Ganduje ya ba ‘dan jarida fili shi kuma ya yi sadaka da shi
Asali: Depositphotos

Malam Nasiru Zango zai kyautar da wannan katon fili a yanzu domin a gina masallaci ko kuma makarantar Islamiyya. ‘Dan jaridar yace idan har ba a samu wasu mabukata ba, zai saida filin domin ayi dawainiyar jinyar wani maras lafiya.

Nasiru Zango yake cewa ko da ya na ‘dan Kano akwai wadanda su ka fi shi cancanta da kyautar fili don haka yake neman masu bukata ya ba su sadaka. Zango ya kuma yi addu’a cewa Allah ya sakawa Gwamna Abdullahi Ganduje da alheri.

Kamar yadda mu ka samu labari, Nasiru Zango wanda yayi fice a babban gidan rediyon nan na Freedom, ya hadu da gwamna Abdullahi Ganduje kwanaki a kasar Saudiyya mai tsarki wajen aikin Umrah.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel