Kungiyar Izala ta ja kunnen zababbun gwamnoni akan neman matan banza

Kungiyar Izala ta ja kunnen zababbun gwamnoni akan neman matan banza

Kungiyar Izalatil bidi’a wa iqamatissunnah reshen jahar Jos ta gargadi sabbin zababbun gwamnonin Najeriya da zababbun yan majalisun dokoki game da neman matan banza bayan darewarsu karagar mulki.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban majalisar Malamai ta kungiyar, Sheikh Sani Yahaya Jingir ne yayi wannan gargadi a garin Jos na jahar Filato a babban taron karama juna sani da kungiyar ta shirya.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana shige-da-fice a Kaduna na sa’o’i 24

“Mun samu ingantattun bayanai bayan kaddamar da wani bincike akan shuwagabannin siyasa, kuma mun gano dalilin da yasa yawancin gwamnoni, ministoci, yan majalisu da manyan jami’an gwamnati basa aikinsu yadda ya kamata shine saboda suna bata lokacinsu tare da matan banza.

“A yanzu haka mun samu labarin ana ta safarar karuwai daga dukkanin sassan Najeriya zuwa babban birnin tarayya Abuja inda za’a rantsar da sabbin zababbun yayan majalisun dokokin Najeriya, karuwan suna zuwa Abuja ne don samun sabbin kwastomomi.” Inji shi.

Daga karshe Sheikh Yahaya Jingir ya tuna musu cewa su sani zasu hadu da Allah Ubangijin talikai a ranar kiyama, kuma zasu yi bayani game da dukkanin ayyukan da suka aikata a duniya, mai kyau ko mara kyau.

A wani labarin kuma shahararren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana goyon bayansa ga dan majalisa Femi Gbajabiamila a kokarinsa na darewa kujerar Kaakakin majalisar wakilai a sabuwar majalisa ta Tara.

Shehin Malamin ya bayyana goyon bayan nasa ga Femi Gbajabiamila ne a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu yayin da suka hadu a farfajiyar Masallacin Makkah dake kasar Saudiyya inda suka tafi zuwa aikin Umarah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel