Hukumar EFCC ta gargadi mutane akan wata sabuwar hanya da barayin mota ke bi wurin satar mota
- Barayin mota sun fito da wata sabuwar hanya ta satar motocin mutane
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gargadi mutane su lura sosai da irin mutanen da suke mu'amala da su musamman masu sayar da motoci
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta na sanar da daukacin al'ummar Najeriya wata sabuwar hanya da barayin motoci su ke bi wurin satar motar mutane.
Hukumar ta shawarci mutane su lura sosai da ababen hawan su, an gano hanyar da barayin ke bi ne, bayan hukumar ta gabatar da bincike akan wani wanda ta kama da laifi mai kamar hakan, mai suna Babatunde Oluwatope Oni wanda aka fi sani da Olu Daniel.
Babatunde wanda ya ke dan asalin Odo Eri, karamar hukumar Yagba da ke cikin jihar Kogi, hukumar ta kama shi da hannu a sata da kuma bayar da takardun karya, wanda wani mai suna Mista Kamoru Yekini ya kawo kara.
Wanda ya kawo karar ya bayyana cewa ranar 16 ga watan Oktoba shekarar 2018, wasu mutane biyu sun zo shagon shi da ke garin Iwo cikin jihar Osun, inda suka nuna bukatar suna son su sayi daya daga cikin motocin da ya ke sayarwa, mai kirar Toyota Matrix.
Bayan sun gama ciniki sun yarda akan kudi N1,580,000, sai suka rubuta mishi cek na banki wanda zai yi amfani da shi ya cire kudin, cek din yana dauke da sunan Rabiu Bamidele Lateef.
"Amma da ya ke Babatunde yana so ya boye niyyar shi ta satar motar, sai ya zo mini a matsayinshi na direban dayan mutumin da suka zo tare. Dayan mutumin ya zo mini a matsayin malami a jami'ar Bowen da ke nan Iwo."
KU KARANTA: Sai na yi nazari kafin na karbi mukami a hannun shugaba Buhari - Dan takarar shugaban kasa
Bayan sun gama dai-dai ta wa, sai mai motar ya je banki zai cire kudin, sai ya tarar da cewar cek din da aka bashi na karya ne.
Dalilin da ya tilasta shi zuwa wurin hukumar yaki da cin hanci da rashawa, domin su taimaka mishi, hukumar ta yi iya bakin kokarinta inda suka samo motar a Abuja, an sayarwa da wata mata akan kudi N1,800,000.
Daga nan hukumar suka matsa bincike har suka kama Babatunde a cikin Abuja.
Bayan an kama Babatunde sai kuma aka kara samun wani mutumi shima ya kawo kara ta satar mota dai-dai da ta Babatunde.
Hukumar dai ta na kara jawo hankalin al'umma akan irin wannan sabuwar hanyar da barayin suka bi don satar motar mutane.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng