Ku daina bin masu laifi a guje, Hukamar kare hadurra ta kasa (FRSC) ta gargadi jami’anta

Ku daina bin masu laifi a guje, Hukamar kare hadurra ta kasa (FRSC) ta gargadi jami’anta

-Bin masu laifi a guje sam ya sabawa dokar aikin Hukumar kare hadurra ta kasa

-Hukumar FRSC ta gargadi jami'anta ne sanadiyar wani hadari da ya auku ranar Juma'a a garin Ibadan sakamakon biyo masu laifi da jami'an hukumar su kayi

Hukumar tayi wannan gargadin ne ranar Assabar da cewa jami’anta su daina bin masu laifi a guje ko ma menene laifin da suka aikata. Jami’i mai kula da sashen ilmantar da jama’a na hukumar, mai suna Bisi Kazeem ne ya bada wannan sanarwa yayinda yake ganawa da manema labarai a Legas ta wayar tarho.

A dai dai lokacin da yake jawabi akan hadarin da ya auku ranar Juma’a a garin Ibadan sanadiyar bin masu laifin da jami’an FRSC su kayi. Kazeem ya shaidawa manema labarai cewa aukuwar wannan lamari yayi matukar batawa Shugaban hukumar tasu rai.

Hukumar FRSC

Hukumar FRSC
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN:Babbar mota ta hallaka wata daliba jim kadan bayan ta biya kudin makaranta a banki

“Hakika Shugaban hukumar tasu, ya nuna bacin ransa bisa ga faruwar wannan hatsari duba da cewa dokar aikinsu ta hana jami’i ya rinka bin mai laifi a guje duk girman laifinsa. Saboda a tsanake ta hanyar lambar abin hawan za’a iya kama mai laifin cikin ruwan sanyi.

“A matsayinmu na hukuma mai aiki akan dokoki irin namu zamu bi kadun wannan lamari, ya zama dole ayi bincike sannan kuma idan aka samu wani jami’inmu da laifi za ayi mashi hukuncin da ya dace dashi,” a fadar Kazeem.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel