Kifa daya kwala: Yadda dan dambe ya sumar da budurwa tsawon kwanaki 2 da naushi daya

Kifa daya kwala: Yadda dan dambe ya sumar da budurwa tsawon kwanaki 2 da naushi daya

A yanzu haka wani fitaccen dan dambe, Abdulrazak Ahmed, wanda aka fi sani da suna Ebola na cikin halin tsaka mai wuya bayan ya shiga hannun hukuma akan zarginsa da ake yi da yunkurin kashe wata budurwa da rikici ya hadasu a gidan dambe.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda sun gurfanar da Ebola a gaban kotun majistri dake Chediya, cikin GRA Zaria a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, inda suka bayyana tuhumar da suke masa da sumar da matar mai suna Farida na tsawon kwanaki biyu.

KU KARANTA: Kungiyar dattawan Arewa zata gudanar da taron gaggawa don tattauna matsalar tsaro

Kifa daya kwala: Yadda dan dambe ya sumar da budurwa tsawon kwanaki 2 da naushi daya

Yan dambe
Source: UGC

Shi dai Ebola mazaunin layin Lafiya ne dake unguwar Kawo Kaduna, a gida mai lamba 230, kuma shekarunsa 24, kamar yadda Dansanda mai shigar da kara, Sajan Mansir Nasir ya bayyana ma kotu.

Sajan Mansir ya bayyana ma kotun cewa a ranar 23 ga watan Maris ne Ebola ya dankara ma Farida Mohammed hannu a gidan dambe dake unguwar sabon gari Zaria, inda har sai da ta suma, kuma ta kwashe kwanaki biyu a bata farfado ba.

Ya kara da cewa sun samu rahoton lamarin ne daga bakin wani matashi da misalin karfe 9 na daren ranar, inda isarsu keda wuya zuwa gidan suka tarar da Farida ba’a cikin hayyacinta ba, daga nan suka garzaya da ita zuwa Asibiti.

Da wannan ne Dansanda Mansir ya nemi kotu ta hukunta Ebola da tsatstsauran hukunci duba da cewa laifin da ya tafka ya saba ma sashi na 224 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Kaduna, sai dai lauyan Ebola, Gabriel Attah ya nemi a bada belin wanda yake karewa.

Bayan sauraron bangarorin biyu ne sai Alkali Abubakar Aliyu Lamido ya bada belin Ebola akan kudi naira miliyan daya, da kuma mutum daya da zai tsaya masa akan kudi N500,000, inda yace ba za’a sakeshi ba sai ya cika sharuddan beli, daga nan kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel