Yanzu Yanzu: Babbar birnin jihar Yobe, Damaturi na karkashin harin Boko Haram

Yanzu Yanzu: Babbar birnin jihar Yobe, Damaturi na karkashin harin Boko Haram

Babbar birnin jihar Yobe, Damaturu, na karkashin harin Boko Haram a yanzu haka. Mazauna yankin maisandari, wajen Damaturu sunce maharan sun zo ne ta yankin kudancin harin sannan suka fara harbi ba kakkautawa.

Daya daga cikinsu, Usaini Maisandari, ya bayyana cewa suna a wajen gidansu lokacin da suka gano yan ta'addan na zuwa yankin cikin motocin hilux.

"Dukkaninmu mun tsere don tsira. kuna jin karar harbin bindiga da na bama-bamai? Ina so kuyi mana addu'a dan Allah," inji shi.

Yanzu Yanzu: Babbar birnin jihar Yobe, Damaturi na karkashin harin Boko Haram

Yanzu Yanzu: Babbar birnin jihar Yobe, Damaturi na karkashin harin Boko Haram
Source: Twitter

Majiyarmu ta Daily Trust ta tabbatar da ganin sojoji dauke da kayayyakin yaki da motocin hilux da dama inda suka tunkari hanyar da yan ta'addan suke.

KU KARANTA KUMA: Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban sashin kashe gobara na Lagas, sun bukaci kudin fansa

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban hukumar sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai, ya ce babban burinsa shine yaga ya inganta jin dadi da kuma lafiyar jami'an sojojin Najeriya.

Babban hafsan sojin ya bayyana hakan jiya Litinin a jihar Bauchi, a lokacin da ya ke gabatar da sabbin gidajen kwana da aka ginawa sojojin a jihar ta Bauchi.

Buratai ya ce a yanzu haka akwai ayyukan da ake gudanarwa a fadin kasar nan, wadanda iya jami'an hukamar soji ne kawai za su amfana da su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel