Shugabancin majalisa: Ndume zai tabbatar da aminci tasakanin bangaren zartarwa da na dokoki - Kungiya

Shugabancin majalisa: Ndume zai tabbatar da aminci tasakanin bangaren zartarwa da na dokoki - Kungiya

Wata gamayyar kungiya mai son ci gaban gwamnati, ta bayyana cewa ya zama dole majalisar dokokin kasar ta guji duk wani hayaniya da ka iya zuwa daga majalisar zartarwa da na dokokin kasar, inda ta bayyana cewa kasar ta fuskanci kalubale a baya a wajen gudanar da ayyuka ta dalilin rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu.

Yayinda take misali da tsayawa takaran Sanata Ali Ndume a matsayin shugaban majalisar dattijai, kungiyar ta jadadda cewa halin dattako da kwarewarsa zai tabbatar da ribar damokradiyyar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi alkawari.

Kungiyar ta kyautata zaton cewa Ndume zai samar da kyakyawar alaka a tsakanin bangaren zartarwa da bangaren dokokin kasar, ta yadda za a samu tarin ci gaba ba tare da an kai ruwa rana ba.

Shugabancin majalisa: Ndume zai tabbatar da aminci tasakanin bangaren zartarwa da na dokoki - Kungiya
Shugabancin majalisa: Ndume zai tabbatar da aminci tasakanin bangaren zartarwa da na dokoki - Kungiya
Asali: UGC

Yayin da yake jawabi ga yan jarida a Abuja, a jiya Litinin, 8 ga watan Afrilu, jagoran kungiyar Amb. Auwal Alhassan Gama ya bukaci shugabancin APC da ta bude filin daga ga wadanda suka cancanci tsayawa takara domin su fafata.

Gama yace: “Taron ta binciko cewa dalili guda daya da yasa gwamnati mai mulki a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata cika alkawarinta ga yan Najeriya ba a fannin kayayyakin more rayuwa da inganta rayuwa ya kasance saboda dalilin rashin jituwa da ke tsakanin majalisar zartarwa da majalisar dokokin kasa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin karin jiragen kasa 2 don sufuri a Abuja-Kaduna

“Wannan yasa an samu kalubale wajen gudanar da ayyukan da aka yiwa kasafin kudi wanda gwamnati tayi yunkurin gudanarwa.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel