Babu mahada tsakanin Buhari da Atiku - BMO ta caccaki Obasanjo

Babu mahada tsakanin Buhari da Atiku - BMO ta caccaki Obasanjo

- Kungiyar BMO ta caccaki Olusegun Obasanjo akan ikirarin da ya yi na cewar Atiku ya zarce shugab Buhari nesa ba kusa ba

- Kungiyar BMO ta ce maganar da tsohon shugaban kasar ya yi tamkar tastuniya ce, wacce ba ta da gindi bare tushe

- Kungiyar ta kuma tariyo yadda Nuhu Ribadu, ya ce cin hanci da rashawa a gwamnatin Obsanjo ya zarce na gwamnatin marigayi Sani Abacha

Kungiyar kafofin sada zumuntar zamani da ke kare muradun Buhari (BMO), a ranar Talata, ta caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo akan ikirarin da ya yi na cewar tsohon mataimakinsa kuma dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zarce shugaban kasa Muhammadu Buhari nesa ba kusa ba.

BMO a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta, Niyi Akinsiju da sakatarenta, Cassidy Madueke a Abuja, ta ce maganar da tsohon shugaban kasar ya yi tamkar tastuniya ce, wacce ba ta da gindi bare tushe.

Kungiyar ya ce: "Gaskiya mun yi mamaki matuka, ace wai wani da ake kallo a matsayin dattijo, ya ci gaba da amfani da matsayinsa wajen kawar da kasar daga turba ta ci gaba.

KARANTA WANNAN: Zamu mayar da dajin Sambisa ya zamo wajen tarihi da yawon bude ido - Rundunar soji

Babu mahada tsakanin Buhari da Atiku - BMO ta caccaki Obasanjo
Babu mahada tsakanin Buhari da Atiku - BMO ta caccaki Obasanjo
Asali: UGC

"Muna sane da cewa a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amfani da ofishinsa na tsawon shekaru hudu wajen aza nagartaccen harsashe na dorewar ci gaban Nigeria, Obasanjo, a matsayin wanda ya rike ragamar Nigeria na tsawon shekaru 8, ya haddasa rudani ta hanyar tsige shugaban majalisar dattijai da gwamnonin jihohi na wancan lokaci da karfin tsiya.

"Sanin kowa ne cewa har shugaban kasa Buhari ya kare wa'adin mulkinsa na shekaru hudu ba a taba kaddamar da dokar ta baci a wata jiha ba, kuma gwamnatinsa ba ta taba yin wani yunkuri na tsige shugaban majaisar dattijai ko gwamnonin jihohi ba.

"Kuma mun tariyo yadda gwamnatin Obasanjo ta kasance mai cike da cin hanci da rashawa da kuma bullo da jakunkunan 'Ghana-must-go' a cikin majalisar tarayya. Haka zaika, 'yan Nigeria ba zasu manta da irin badakalar da aka tafka a fannin wutar lantarki karkashin Obasanjo ba, tare da kuma amfani da biliyoyin kudaden kasar wajen gina dakin karatun shugaban kasa Obasanjo."

Kungiyar ta kuma tariyo yadda tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Mallam Nuhu Ribadu, ya ce cin hanci da rashawa a gwamnatin shugaba Obsanjo ya zarce na gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha nesa ba kusa ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel