An shiga fargaba a majalisar dokokin Jigawa kan yunkurin tsige kakakin majalisa

An shiga fargaba a majalisar dokokin Jigawa kan yunkurin tsige kakakin majalisa

- Ana rade-radin cewa ana nan ana kulle-kulle a majalisar dokokin jihar Jigawa don ganin an tsige kakakin majalisar jihar mai ci

- An tattaro cewa ana ta gudanar da tattaunawa a jihar da jihohin Kano da Bauchi da ke makwabtaka da jihar

- Wa’adin mulkin wannan majalisa mai ci zai kare a ranar 10 ga watan Yuni

Rahotanni sun kawo cewa an shiga halin dar-dar a majalisar dokoki jihar Jigawa kan wani makirci da ake kullawa don tsige kakakin majalisar dokokin jihar, Idris Garba, wanda aka fi sani da Kareka.

Wa’adin mulkin wannan majalisa mai ci zai kare a ranar 10 ga watan Yuni, 2019.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ana ta gudanar da tattaunawa a jihar da jihohin Kano da Bauchi da ke makwabtaka da jihar. Lamarin ya sha kan ayyukan zababbun mambobin majalisar dokkin jihar.

An shiga fargaba a majalisar dokokin Jigawa kan yunkurin tsige kakakin majalisa
An shiga fargaba a majalisar dokokin Jigawa kan yunkurin tsige kakakin majalisa
Asali: UGC

Akwai wasu rahotanni da ke nuna cewa makircin da ake shiryawa na tsige kakakin majalisar mai ci, Isa Idris, kan zargin gazawa na samun goyon bayan bangaren zartarwa.

KU KARANTA KUMA: APC ba mallakarka ba ce: Zababbun Sanatoci sun mayarwa Tinubu Martani

A lokacin da aka tuntube su, masu magana da yawun gwamnan da na majalisar dokokin jihar, Bello Zaki da Babangida Usman Hadejia, sun karyata samun masaniya akan wani shiri na maye gurbin kakakin majalisar mai ci.

Ku tuna cewa an tsige tsohon kakakin majalisar a watan Janairu 2017 kan abunda mambobin majalisar suka kira da wofantar da karfin mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel