Farfesa A. D Kankia ne Mukaddashin VC na Jami’ar Dutsin-Ma

Farfesa A. D Kankia ne Mukaddashin VC na Jami’ar Dutsin-Ma

Hukumar Jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da ke cikin jihar Katsina, ta bada sunan Farfesa Aminu Ɗalhat Kankia a matsayin shugaban makarantar na rikon kwarya.

Katsina Post ta rahoto cewa an bada sunan Farfesa A. D Kankia a matsayin wanda zai jagoranci ragamar jami’ar ne har zuwa nan da watanni 6 masu zuwa bayan cikar wa’adin shugaban jami’ar wanda ke kan kujera a yanzu.

Kamar yadda labari ya zo gare mu a jiya, wa’adin Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi wanda ke rikon kwarya ya cika ne a cikin ‘yan kwanakin nan, bayan yayi shekaru biyu da rabi a matsayin mukaddashin shugaban jami’ar.

KU KARANTA: Gwamnan Katsina Masari ya gana da Mataimakin Shugaban kasa

Farfesa A. D Kankia ne Mukaddashin VC na Jami’ar Dutsin-Ma
Farfesa Aminu Ɗalhat Kankia zai rike FUDMA na wani lokaci
Asali: Instagram

Doka da sharudan jami’o’i na NUC sun gindaya cewa babu yadda za ayi mutum yayi fiye da shekaru biyu da rabi yana mai rikon kwarya a jami’ar Najeriya. Wannan ya sa dole Farfesa A.H Bichi ya bada wuri domin a nada wani shugaban.

Farfesa Kankia, kwararre ne a bangaren koyar da lissafi kuma shi ne shugaban sashen koyar da kimiyya, haka kuma shi ne babban Darektan tsangayar SOGAPS kafin a aika sunan sa. Ana sa rai cewa zai rike kujerar ne na wani lokaci.

Jami’ar tarayyar dai ta dade babu wani takamaimen shugaba tun bayan da hukumar makarantar ta tsige Farfesa Abdu Haruna Kaita daga matsayin VC mai kula da jami’ar kwanaki bayan ya samu matsala da Hajiya Maraliya Zayyan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel