Zaben Kaduna: Masu kula da zaben Najeriya sun nuna APC tayi barna

Zaben Kaduna: Masu kula da zaben Najeriya sun nuna APC tayi barna

Wasu daga cikin kungiyoyin da su ka zura idanu a zaben gwamnan jihar Kaduna da aka yi kwanan nan, sun nuna cewa an tafka aikin Ma-sha-a a wannan zabe da jam’iyyar APC mai mulki ta samu nasara.

Sai dai kuma duk da irin ba dai-dai din da aka tafka a zaben, wadannan kungiyoyi sun nuna cewa ba za su nemi a sake gudanar da wani sabon zaben gwamna a jihar ba. Gwamna Nasir El-Rufai ne dai ya samu zarcewa a kan karagar mulki.

Farfesa Banake Sambo na kungiyar nan ta “Initiative for the Promotion of Civic Obligation and Sustainable Peace” ne ya jagoranci sauran wadannan kungiyoyi irin su kungiyar The Integrity Friends for Truth and peace initiative.

Wadannan kungiyoyi da su ka lura da zaben gwamna a jihar sun ce an samu wuraren da sojoji su ka rika cin zarafi tare da muzgunuwa jama’a. Banake Sambo ya kuma ce a wasu wuraren, an yi amfani da kudi wajen sayen kuri’a.

KU KARANTA: Mawakan Hausa sun nemi Buhari ya duba lamarin zaben Kano

Zaben Kaduna: Masu kula da zaben Najeriya sun nuna APC tayi barna
Masu sa ido a zaben Najeriya sun ce an yi murdiya a Kaduna
Asali: UGC

Garuruwan da aka yi fama da matsalar sayen kuri’ar jama’a sun hada da Garin Ikara, Kubau da kuma kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da kudu. A wadannan yankuna, jam’iyyar APC ta samu tarin kudi’a inji kungiyoyin.

Bayan haka kuma, wannan kungiya ta Initiative for the Promotion of Civic Obligation and Sustainable Peace tace sam ba ayi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a na Card Reader a kananan hukumomi 10 na jihar ba.

Wananan kananan hukumomi su ne: Giwa, Zaria, Sabon-Gari, Ikara, Lere, Igabi, Soba, Kaduna ta Arewa da kuma cikin karamar hukumar Kaduna ta kudu. Har wa yau, B. Sambi yace an sace akwatin zabe a cikin yankin Birnin Gwari.

Kungiyoyin masu zaman kan su, sun ce inda sojoji su kayi ta’adi su ne cikin Garuruwan Ikara irin su; cikin Birnin Ikara, Fala, Sayasaya, Kurmin Kogi, Rumi Auchan, Kuya, Paki, Jamfalan da kuma Saulawa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel