Duniya ina za ki da mu: An sake tsintar wata gawa a cikin rijiya a jihar Filato

Duniya ina za ki da mu: An sake tsintar wata gawa a cikin rijiya a jihar Filato

Sake tsintar wata gawa a cikin rijiya a safiyar ranar Talata ya sake haddasa wani tashin hankali da zaman dar-dar a tsakanin Musulmai da Kirista na al'ummar garin Dutse Uku, karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar Filato.

A watan Nuwambar shekarar da ta gabata ne rundunar soji ta gano gawar tsohon shugabanta Manjo Janar Mohammed Idris Alkali (rtd.), wanda rahotannin suka bayyana cewa ya bace a cikin wani sarkakken yanayi. Sai dai an gano gawarsa a cikin wata rijiya da ke dajin kauyen Guchwet, gundumar Shen, karamar hukumar Jos ta Kudu, bayan da rundunar sojin ta tsananta bincike.

Daily Trust ta ruwaito cewa mamacin da aka tsinci gawar ta sa mai shekaru 25, an kashe shi ne a daren ranar Litinin inda aka jefar da shi a cikin rijiyar. Bayan tsintar gawar ta sa a jiya, rudani ya mamaye garin musamman bayan da matasa suka shirya gudanar da zanga zanga, amma aka dakile su kafin yin hakan.

KARANTA WANNAN: Za a haddasa babban rikici a Nigeria idan har aka murde zaben Kano - Babatope

Duniya ina za ki da mu: An sake tsintar wata gawa a cikin rijiya a jihar Filato
Duniya ina za ki da mu: An sake tsintar wata gawa a cikin rijiya a jihar Filato
Asali: Twitter

Wani da lamarin ya auku gabansa da ke sayar da burkutu a sha-tale-talen Tina ya ce mamacimn yaron wani mai gadi ne da ke aiki a majami'ar Christ in Nations da ke yankin.

Mai magana da yawun rundunar soji da ke atisayen Safe Haven, Manjo Adam Umar, ya ce gano gawar ya haddasa rundani da hargowa a tsakanin jama'ar yankin.

Ya ce: "gaba daya yankin na cike da mutanenmu, jami'an 'yan sanda sun tafi da gawar, yanzu dai komai ya koma dai-dai."

Haka zalika, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, Tyopev Terna, ya tabbatar da cire gawar daga cikin rijiyar inda ya ce tuni rundunar ta soma gudanar da bincike.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel