Aisha Buhari ta ari bakin mijinta: Yayan jam’iyyar APC kadai zamu raba ma mukamai

Aisha Buhari ta ari bakin mijinta: Yayan jam’iyyar APC kadai zamu raba ma mukamai

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta shawarci gwamnatin jam’iyyar APC da kada ta kuskura ta sanya bare a cikin wadanda zata raba ma mukaman siyasa, matukar ba yayan jam’iyyar APC bane.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Aisha ta bayyana haka ne a yayin wani liyafar cin abinci da ta shirya a garin Daura na jahar Katsina don murnar samun nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda tace lokaci yayin daya kamata a sakanka ma yan jam’iyya.

KU KARANTA: Kaico! Malamin Islamiyya ya murde wuyan dalibinsa a jahar Taraba

Aisha Buhari ta ari bakin mijinta: Yayan jam’iyyar APC kadai zamu raba ma mukamai
Aisha da Buhari
Asali: Facebook

Liyafar cin abincin da aka shiryashi a gyararren filin wasanni da motsa jiki na garin Daura ya samu halartar kungiyoyin matasa da mata, yan siyasa, manyan baki da kuma magoya bayan jam’iyyar APC daga sassan daban daban na jahar.

Cikin wata sanarwa da hadimin Aisha Buhari ta fuskar watsa labaru Suleiman Haruna ya fitar, yace kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya fayyace wadanda ya kamata a nada mukaman siyasa, kuma sune yayan jam’iyya kadai.

Don haka tayi kira ga APC da tayi biyayya ga kundin tsarin mulkin nata, haka nan Aisha ta bayyana farin cikinta da goyon bayan da jama’a suka baiwa APC a yayin zaben shugaban kasa daya gabata, inda ta bada tabbacin gwamnatin zata cigaba dagewa akan ayyukan da ta sanya a gaba.

Da yake nasa jawabi, Ministan sufurin jirgin sama, Hadi Sirika ya jinjina ma duk wadanda suka zabi shugaban kasa Buhari a karo na biyu, inda ya sake jaddada cewa tazracen Buhari na tafe da ayyukan cigaba da dama.

Daga karshe ya yaba ma uwargida Aisha game da yadda take jan mata da matasa a jiki tun daga lokacin da aka fara yakin neman zabe, wanda hakan ne ya sabbaba miliyoyin kuri’un da Buhari ya samu a zaben shugaban kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel