An bankado 'yan majalisun tarayya na APC guda 4 da ke amfani da takardun bogi a Bauchi

An bankado 'yan majalisun tarayya na APC guda 4 da ke amfani da takardun bogi a Bauchi

Wata kungiya da aka kafa domin bunkasa rayuwar mata marasa galihu da kananan yara, (Initiative for Vulnerable Women and Children (SIVWOC), ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yiyuwar rasa wasu kujerun majalisun tarayya na jam'iyyar APC saboda kakabawa jama'a 'yan takarar da basu cancanta ba, uwa uba masu amfani da takardun bogi a zaben ranar Asabar da za a yi a jihar Bauchi.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Safiya Abdullahi Bauchi, kungiyar ta yi tuni da cewa zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC ta gudanar a jihar Bauchi na cike da kura-kurai, tauye hakkin shari'a, kakabawa jama'a zabin da basa so, nuna karfin ikon mulki da kuma zabawa jama'a mazanbatan 'yan takara.

A cewer sanarwar, wannan zaben fitar da gwani, ya haddasa shakku a tsakanin mabiyan jam'iyyar, ba a jihar kadai ba, hatta a jihohi irinsu Zamfara, Rivers da kuma ita kanta Bauchi, inda har suka gano wasu 'yan takarar kujerun majalisun tarayya guda hudu masu amfani da takardun karatu na bogi da kuma karya kan ranakun haihuwa.

KARANTA WANNAN: Asiri ya tonu: Yadda INEC ta sanya sunan matattu miliyan 1 a cikin rejistar masu zabe - PDP

Gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abdullahi Abubakar

Gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abdullahi Abubakar
Source: Depositphotos

A cikin cikakken bayanin da kungiyar SIVWOC ta gabatar, ta gabatar da rahoton binciken da ta yi akan wadannan mutane, a cikin wasikar da ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ga cikakkar wasikar:

1. HALLIRU DAUDA JIKA (Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Darazo/Ganjuwa mai ci a yanzu, kuma dan takarar sanatan mazabar Bauchi ta kudu a majalisar dattijai)

Dangane da Halliru Dauda Jika, akwai sarkakiya a lamarinsa. Misali, a bayanan da ya wallafa na matsayinsa na dan majalisar tarayya, an samu cewa ya kammala karatunsa na farko da matakin karamar diploma a fannin 'Civil Engineering' daga makarantar koyar da sana'o'i da kere-kere ta Kaduna a shekarar 2015. Sai dai, a bayanansa da ke kunshe cikin takardar INEC mai lamba CF001 ta shakarar 2015 da 2019 ya nuna cewa ya kammala karatunsa na diploma a shekarar 2004.

Kari a kan hakan, ya bayyana cewa ya zana jarabawar WAEC a shekarar 1999 (kamar yadda yake kunshe a bayanansa na majalisar tarayya), yayin da a takardar INEC mai lamba CF001 ta shekarar 2015 da 2019 ya bayyana cewa ya zana jarabawarsa ta kammala makarantar sakandire (WAEC) a shekarar 2000.

Wani abun mamaki dangane da lamarin Halliru Dauda Jika shine, yadda aka samu sabani a ranakun haihuwarsa. Bayanin da ke kunshe a cikin takarar INEC ta shekarar 2015 da 2019 ya bayyana cewa, a cikin takardar bayanansa ta nemam aiki (CV) ya yi ikirarin cewa an haife shi a ranar 18 ga watan Satumba, 1976, yayin da a cikin takardarsa ta kammala makarantar firamare, ya yi ikirarin cewa an haife sa a ranar 10 ga watan Yuli, 1979. Haka zalika a cikin takardar kotu ta rantsuwar shekaru a madadin mahaifinsa, ya yi ikirarin cewa an haife sa a ranar 17 ga watan Afrelu, 1976.

A takarar jarabawarsa mai kwanan wata, Yuli 2014, kwanan watan haihuwarsa ya kasance ranar 17 ga watan Afrelu, 1979. A takaicen takaitawa, yana da ranakun haihuwa mabanbanta har guda hudu. Hakika wannan zamba ce tsagwaronta!

Wani abun daga hankali shine yadda aka gano cewa takardar jarabawarsa ta WAEC wacce aka sanya a cikin kundin bayanansa na INEC mai lamba CF001, wacce ta nuna cewa ya samu nasarar tsallake darasin Hausa da 'Credit' kawai, yayin da ya ke da makin 'Pass' a darussa shida, sai kuma ya fadi a darasin zane (Technical Drawing) da kuma samun matsala a darasin sarrafa katako (Wood Work).Abun daukar hankalin a nan shine, ya yi ikirarin cewa ya kammala diploma a fannin 'Civil Engineering' daga makarantar koyar da sana'o'i da kere-kere ta Kaduna, tambayar anan ita ce; Shin zai iya samun gurbin karantar fannin 'Civil Engineering' a KADPOLY ko kuma dai makarantar koyar da sana'o'i da kere-kere ta Kaduna ta bashi gurbin yin karatu a fannin 'Civil Engineering' alhalin yana da makin 'Credit' a darasin Hausa kawai da kuma makin 'Pass' a darussa shida, tare da faduwa darasin zane da kuma rashin tabbas a darasin sarrafa katako? Kowa ya san wannan amsar "A'a" ce, hakan ba zai taba yiyuwa ba.

2. MOHAMMED GARBA GOLOLO (Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gamawa, a majalisar wakilan tarayya, mai ci a yanzu, kuma dan takarar wannan kujera a karkashin jam'iyyar APC)

Sunan Mohammed Garba Gololo ba boyayye bane ga 'yan Nigeria, musamman idan aka tariyo yadda aka same sa dumu-dumu a zargin da aka yi masa na cin zarafin mata a lokacin da aka tura sa wani aiki kasar Amurka. Wannan mutumin shine kuma ya yi rantsuwa da cewar ya kammala karatun digiri daga jami'ar jihar Legas (LASU) a bangaren ilimin kasuwanci (Bsc Business Administration) da kuma (MBA Business Management) a shekarar 2002 da kuma 2005. Kwakkwaran bincike da nazari kan wadannan matakan karatun ya sanya kokonto akan gaskiya ko akasinta akansu.

A matsayinmu na 'yan kasa na-gari, wadanda suke ganin kwazon shugaban kasa Muhammadu Buhari a yankurinsa na yaki da cin hanci da rashawa, mun gudanar da bincike domin sanin hakikanin gaskiya kan matakan ilimin dan majalisar. A karshe dai binciken namu ya haifar da d'a mai ido. Jami'ar jihar Legas, a cikin wata takarda mai lamba LASU/REG.STUM/147, mai kwanan wata, 1 ga watan Nuwamba, 2018, ta maido mana da cikakken bayani kan bukatar da muka gabatar mata na son sanin sahihancin takardun karatun da Mr Gololo ya ke amfani da su a kundin INEC mai lamba CF001. Jami'ar ta ce takardun na bogi ne, ba ta hannunta suka fito ba, inda har ta fayyace cewa Mr Gololo bai yi karatu a fannonin biyu da ya ce ya yi a jami'ar ba. Hade da wannan wasikar tamu, akwai kwafi na takardar da jami'ar ta turo mana domin kaima ka tabbatar da gaskiyar binciken da kanka.

Ya shugaban kasa, muna da kyakkyawan yakinin cewa APC za ta rasa kujerar mazabar Ganjuwa a majalisar tarayya, idan har jam'iyyar adawa ta shigar da kara kotu ko da kuwa APC ce ta yi nasara a zaben, sakamakon zargin amfani da takardun bogi, jam'iyyar adawa na iya samun nasara a kotu.

3. ABUBAKAR DALHATU ABDULLAHI (Dan takarar kujerar majalisar wakilan tarayya a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, karkashin jam'iyyar APC)

Mr. Abubakar Dalhatu Abdullahi, wanda dan koyo ne a fagen siyasa, zamu iya cewa an tsayar da shi takara ba da son al'ummar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa ba. Rahotanni sun bayyana cewa ya kasance yana da zama da iyalansa a wata jihar mai nisa da jihar Bauchi, watau jihar Legas, inda ya ke lekowa mazabar da ake so ya wakilta sau daya ko biyu a shekara.

Shi wannan mutumin, ya yi rantsuwa da cewar ya kammala karatun Firamare daga makarantar Kantana-Dull a shekarar 1980. Sai dai binciken da muka yi ya tabbatar da cewa ita kanta makarantar Firamdare ta Kantana-Dull an kafa ta ne a shekarar 1978, inda aka fara budeta da dalibai 45, tare da Mallam Adamu Jumba a matsayin shugabanta. A tsakanin shekarun 1970, ana daukar shekaru tara kafin a kammala karatun firamare. Abun tambayar a nan shine; ta ya za ayi a ce makarantar da aka bude ta a shekarar 1978, dalibai su kammalata bayan shekaru biyu da fara karatu?. Babu tantama takardar kammala firamarensa ta bogi ce. Daga nan zamu fahimci cewa tunda har takardar kammala firamaren da ya gabatar ta bogi ce, to kuwa sauran takardun karatunsa da ya gabatar na bogi ne suma.

Mr. Abdullahi bai gabatar da wata takardar shaidar zana jarabawar WAEC ko makamanciyarta kamar yadda ya dace ya yi a cikin kundin bayanansa na INEC ba. Da wannan ya zama hujja na cewar akwai cuwa-cuwa a tsakaninsa da jami'an jam'iyyar APC da suka tantance shi, idan har ma an gudanar da tantancewar. Ya kamata ce duk wani jami'in jam'iyya wanda ya san aikin da yake yi, ya gano cewa wannan mutumin mazanbaci ne, wanda bai cancanci tsallake wannan tantancewar ba, amma ba ayi hakan ba.

Haka zalika, Mr Abdullahi ya ce ya kammala karatun diploma daga jami'ar jihar Legas (LASU) a fannin ilimin harshen larabci da harkokin Musulunci a zangon karatu na shekarar 2004/2005. Amma ta ya za ayi Mr Abdullahi wanda bai mallaki takardar WAEC ba ace har ya samu gurbin karatun diploma a jami'ar jihar Legas? Domin tabbatar da tsantsar zamba cikin aminci ta wannan mutumin, binciken da muka yi ya bayyana cewa hukumar da ke kula da manyan makarantu ta kasa (NUC) a shekarar 2004 ta sanar da dukkanin jami'o'in Nigeria cewa ta haramta masu daukar darussan matakin diploma. Ko ta ya za ayi a ce Mr. Abdullahi ya kammala karatunsa na diploma a shekarar 2005? Shin jami'ar jihar Legas ta taba kammala zangon karatun Diploma a cikin shekara daya kacal? Kowa ya san amsoshin tambayoyin nan "A'a" ce. A takaice dai ta tabbata Mr Abdullahi babban makaryaci ne kuma mazambaci wanda bai cancanci zama karkashin inuwar jam'iyyar APC ba balle har ya samu damar yin takarar wata kujerar zabe. Kamar kowa, duk wata kuri'a da za'a kada a madadinsa za ta tashi a banza, har sai idan zai cusa rashawa a cikin shari'ar kotun. Tabbas idan aka bi ta daga-daga ya cancanci zaman wakafi.

4. IBRAHIM MOHAMMED BABA (Dan majalisa mai wakiltar mazabar Katagum a majalisar tarayya kuma dan takarar wanna kujera karkashin jam'iyyar APC)

Bisa kyakkyawan nazari da muka yi akan bayanan Ibrahim Mohammed Baba da ke kunshe a kundinsa na majalisar tarayya da kuma wanda ya ke kunshe a kundinsa na INEC mai lamba CF001 na shekar 2015 da na 2019, mun gano cewa akwai banbance banbancen bayanai da dama.

Misali, a bayanansa da ke kunshe a kundinsa na majalisar tarayya, ya yi ikirarin cewa ya samu wadannan takardu tare da kwanan watansu:

Bin diddigin bayanansa da ke kunshe a kundinsa na majalisar tarayya, ya yi ikirarin cewa ya kammala karatunsa na matakin diploma daga makarantar koyar da sana'o'i da kere-kere ta Kaduna a shekarar 1994, yayin da bayanin sakamakon karatunsa na KADPOLY da ke kunshe a kundinsa na INEC mai lamba CF001 na shekarar 2015 ya bayyana cewa ya kammala karatunsa a shekarar 2000.

Kari da hakan, dangane da takardarsa ta kammala digiri a fannin 'Bsc Accounting', bayanin da ke kunshe a kundinsa na majalisar tarayya ya bayyana cewa, ya kammala karatunsa na fannin 'Bsc Accounting' a shekarar 2006, yayin da kundinsa na INEC mai lamba CF001 na shekar 2015, ya bayyana cewa ya kammala karatun ne a 2008.

Dangane da matakin karatun digirinsa na biyu, kamar yadda yake kunshe a cikin kundin bayanansa na majalisar tarayya, ya yi ikirarin cewa ya kammala a fannin sha'anin kudade (Finance) a shekarar 2008, ya yin da a kundin bayanansa na INEC mai lamba CF001 na shekarar 2015 ya yi ikirarin cewa ya yi digiri na biyu a fannin sha'anin tattalin kudade (Financial Economics), kuma ya kammala a shekarar 2011.

Abun mamakin anan shine; a bayansa da ke cikin kudinsa na INEC mai lamba CF001 na shekarar 2015 ya zayyana cewa takardun karatunsa da suka hada da, FLSC, WAEC, ND, B.Sc, MSC, amma a kundin bayansa na INEC mai lamba CF001 na shekarar 2018 ya lissafa FSLC da WAEC a matsayin matakan karatunsa kawai.

Tambayar da take bukatar amsa a nan ita ce, shin yana da matsala a takardunsa na kammala makarantun gaba da sakandire, da ya yi amfani da su har ya zama mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilan tarayya kan binciken harkokin jama'a, da yanzu ya gaza lissafa su a cikin kundin bayansa na INEC mai lamba CF001 na shekarar 2018? Mr Ibrahim kamar sauran takwarorinsa da muka ambata a sama, babban makaryaci ne kuma mazanbaci, wanda zabarsa zai jawo asarar kuri'u ne kawai. Shime idan aka bi ta daga-daga ya cancanci zaman wakafi la'akari da cewa ya yi rantsuwa akan karya.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa akwai wata babbar ambaliya da ke daf da yin tsiri ta wanke tare da yin awon gaba da duk wata nasara ta jam'iyyar APC a jihar Bauchi, saboda sam ba a gudanar da zabukan fitar da gwani a Bauchi ba. Gwamnan jihar ya yi amfani da karfin ikonsa ya kakabawa al'ummar jihar mutanen da ba sa so, kuma tabbas APC ce za ta sha kunya idan har aka bar wannan zanbar ta tafi ba tare da daukar mataki ba.

Kungiyar ta ce mata da kananan yara sune a kullum ke shan bakar wahala a hannun gurbatattu kuma mazanbatan shuwagabanni. Wannan ne ma babban dalilin da ya sa suka damu matuka akan irin zanbar da ake tafkawa a jihar Bauchi, musamman ganin ta shafi jam'iyyarka ta APC.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel