Ku rubuta ku aje: Kowacce karamar hukuma a Kaduna sai ta samu babbar makaranta - El-Rufai

Ku rubuta ku aje: Kowacce karamar hukuma a Kaduna sai ta samu babbar makaranta - El-Rufai

- Gwamna Nasir El-Rufai ya ce gwamnatin jihar ta batar da makudan kudade wajen ganin ta bunkasa fannin ilimi a Kaduna tun bayan shigarsa ofis a matsayin gwamnan jihar

- El-Rufai ya kuma sha alwashin gina wani bangare na kwalejin Nuhu Bamali a garin Soba, domin saukakawa al'ummar yankin da ke da sha'awar yin karatu a kwalejin

- Haka zalika, gwamnan, ya ce zai tabbata an samar da babbar makaranta a kowacce karamar hukuma da ke jihar Kaduna domin bunkasa ilimi a jihar

Gwamna Nasir El-Rufai ya ce gwamnatin jihar ta batar da makudan kudade wajen ganin ta bunkasa fannin ilimi a Kaduna tun bayan shigarsa ofis a matsayin gwamnan jihar, a yayin da ya kuma yi alkawarin yin duk mai yiyuwa na ganin ya daga darajar fannin a wa'adin mulkinsa na biyu.

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a garin Soba, shelkwatar karamar hukumar Soba, a wani taron masu ruwa da tsaki a ranar Laraba, ya sha alwashin gina wani bangare na kwalejin Nuhu Bamali a garin Soba, domin saukakawa al'ummar yankin da ke da sha'awar yin karatu a kwalejin.

A jawabin da ya gabatar a yayin taron, El-Rufai ya kuma sha alwashin cewa zai tabbata an samar da babbar makaranta a kowacce karamar hukuma da ke jihar Kaduna domin bunkasa ilimi a jihar.

KARANTA WANNAN: Asiri ya tonu: Yadda na murde zaben ANPP a 2003 domin Buhari ya yi nasara - Bafarawa

Ku rubuta ku aje: Kowacce karamar hukuma a Kaduna sai ta samu babbar makaranta - El-Rufai

Ku rubuta ku aje: Kowacce karamar hukuma a Kaduna sai ta samu babbar makaranta - El-Rufai
Source: Depositphotos

Sai dai gwamnan ya shawarci jama'ar karamar hukumar Soba da su rungumi ilimin zamani domin basu damar bayar da gudunmowarsu ta fuskar aikin gwamnati.

Ya ce abun damuwa ne matuka, yadda har yanzu, ba a taba samun wani babban sakatare daga karamar hukumar ba.

A cewar gwamnan, duniya a yanzu ta canja kasancewar babu wani bangare na rayuwa da mutum zai dauka wanda babu bukatar ilimi a ciki, "wannan ne ya sa na mayar da ilimi abu mai muhimmanci a gwamnatina."

Haka zalika El-Rufai ya jaddada cewa yana da yakinin zabe mai zuwa zai kasance cikin lumana ba tare da tashin hankali ba kasancewar babban mashawarci na kasa kan tsaro, Janar Babangida Monguno (mai ritaya) ya kaddamar da wani shiri na ganin an gudanar da zaben lami lafiya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel