Uwargidar Jonathan ta nunawa Kotu yadda ta samu dukiyar ta
Tsohuwar Uwargidan Najeriya, Dame Patience Jonathan ta bayyanawa Duniya yadda ta samu dukiyar ta. Patience Jonathan tayi wannan jawabi ne ta bakin Lauyoyin da ke kare ta a gaban Kotu a jiya.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar The Nation, Dame Patience Jonathan ta gabatar da bidiyoyi 5 domin nunawa kotu yadda ta mallaki dukiyar da gwamnatin Najeriya ke neman karbe mata ta hannun hukumar EFCC.
Lauyoyin Mai dakin tsohon shugaban kasa Jonathan sun haskawa Alkali mai shari’a Mojisola Olatoregun na babban kotun tarayya da ke Legas bidiyoyin da za su gaskaka maganar da tsohuwar Uwargidan ta Najeriya ta ke yi.
KU KARANTA: An hurowa Magu wuta ya fara binciken Sanatan da ya tsero APC
A shekarar bara ne kotu ta bada umarni a soma rufe asusun Dame Patience bisa zargin da EFCC ta ke yi game da hanyar da aka mallaki wannan kudi. Yanzu ma ta kai Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya nemi kotu ta rufe asusun na din-din-din.
Daga cikin bidiyoyin da aka nunawa kotu, akwai wanda aka ga yadda Matar Jonathan ta ke samun kudi ta wani makeken kamfanin ta da ke harkar gyaran kayan gida. Sannan kuma an ga yadda Jonathan ke samun kudi da kasuwancin otel.
KU KARANTA: Hukumar EFCC ba ta shigo cikin gdana ba – inji Alkalin-alkalai
Akwai wasu bidiyoyi da Lauyoyin Jonathan su ka haska a kotu inda aka ga yadda Mai dakin tsohon shugaban kasar tana tallafawa ‘ya ‘ya mata da kayan abinci da sauran su, domin nunawa Kotu yadda ta samu tarin dukiyar ta.
Yanzu dai Lauyan Jonathan, Mike Ozekhome (SAN) yana adawa da baran da EFCC ta ke yi na ganin an rufe asusun tsohuwar Uwargidan kasar. Ifedayo Adedipe (SAN) yana cikin masu kare Jonathan inda za a cigaba da shari’a yau.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tana zargin matar tsohon shugaban Kasar da mallakar Dala miliyan 8.4 da kuma wasu Naira biliyan 7.4 ta hanyoyin da ba su dace ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng