Wata Marainiya tayi nasara a gasar musabakar Al-Kur’ani a Gombe

Wata Marainiya tayi nasara a gasar musabakar Al-Kur’ani a Gombe

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata Marainiya mai shekaru 16 a Duniya ce tayi nasara a gasar karatun Al-kur’ani da aka yi wannan shekarar a garin Gombe. A jiya Asabar ne aka kamalla wannan gasar.

Wata Marainiya tayi nasara a gasar musabakar Al-Kur’ani a Gombe

Gwamnan Gombe ya rabawa wadanda su ka lashe Musabakar Al-Kur’ani kudi
Source: UGC

Zainab Mahmud wanda tana cikin wadanda su ka wakilici jihar Adamawa ce ta zo ta 1 a gasar a rukunin 'yan mata. Zainab, Marainiya ce mai shekaru 16 da haihuwa. Zakakuran mahadda 377 ne su ka shiga wannan gagarumar gasa.

A rukunin maza kuma, Tijjani Muhammad Gwani, wanda ya fito daga jihar Yobe ne yayi nasara. Sarkin Gombe, mai martaba Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III ya karrama wadanda su kayi nasarar a madadin Sarkin Musulmi.

Wadanda su ka zo na farko sun samu kyautar N500, 000 da kuma motoci daga hannun gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo. Bayan nan kuma wadannan Mahaddata za su sauke farali a hajjin shekarar nan a kasa mai tsarki.

KU KARANTA: 'Daliban Najeriya sun karbi Miliyoyi a hannun Shugaban kasa Buhari - ASUU

Gwamnan Gombe ya kuma bada kyautar kudi Naira miliyan 1 ga wata Baiwar Allah ‘yar shekara 8 da ta haddace Al’kur’ani kaf tare da Tajwidi. Wannan yarinya mai suna Basira Ahmed, ta fito ne daga Jihar Edo da ke Kudancin Najeriya.

An soma gasar ne a ranar 27 na watan Disamba, inda aka kamalla a jiya. Wannan ne karo na 33 da aka gudanar da musabakar Al-kur’ani na kasa a Najeriya. An samu mahaddata daga jihohi 33 a wajen wannan katafariyar musabaka.

Sulaiman Hassan Zarma, shi ne ya wakilici shugaba Muhammadu Buhari a wajen taron. Shugaban kasar, ta bakin Ministan ya nemi jama’a su zama masu kawo zaman lafiya da kuma hakuri da juna a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel