‘Yan Boko Haram sun sa Bayin Allah da-dama sun bar Garuruwan Borno

‘Yan Boko Haram sun sa Bayin Allah da-dama sun bar Garuruwan Borno

Mun samu labari cewa akalla mutum 10, 000 sun tsere daga wasu Garuruwa a jihar Borno saboda hare-haren Boko Haram kwanan nan. Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai a karshen makon jiya.

‘Yan Boko Haram sun sa Bayin Allah da-dama sun bar Garuruwan Borno

Mutanen Baga sun fake a cikin Monguno da Maiduguri
Source: UGC

A cikin makon nan, mutane da dama sun bar gidajen su a Garuruwa irin su Baga, Doro, Mike 4 da wasu kauyuka a cikin karamar hukumar Kukawa. Mafi yawan wadanda su ka tsere, sun fake ne a cikin Maiduguri da kuma Monguno.

Shugabar jami’ar SEMA mai bada gajin gaggawa a jihar Borno, ta bayyana cewa, mutane akalla 7000 su ka tsero zuwa garin Monguno, yayin da mutum kusan 3000 su ke labe a sansanin ‘yan gudun hijira a cikin babban birnin Maiduguri.

KU KARANTA: Rudunar Sojoji sun yi damarar fatattakan Boko Haram daga Baga

Hajiya Yabawa Kolo wanda ke lura da hukumar SEMA ta tabbatar da cewa mafi yawan wadanda su ka baro gidajen su zuwa Monguno, manoma da kuma masunta. Kwanaki Sojoji su ka fatattaki ‘yan Boko Haram daga cikin Monguno.

Jaridar Daily Trust ta dai bayyana cewa bayan wadannan mutane sama da 10, 000 da su ke cikin Borno, akwai kuma jama’a da-dama da su ka tsere daga Borno zuwa jihar Yobe. Har yanzu haka dai akwai kuma jama’an da ke fake a daji.

Yanzu haka dai akwai mutane fiye da 250, 000 a garin Monguno inda mafi yawan su, ‘yan gudun hijira ne. Wannan ya sa gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya kai ziyara zuwa yankin kwanan nan domin raba abinci da kayan agaji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel