Ranar hisabi: An yiwa Saraki ihu a wurin gangamin kamfe a garin Ilori (Bidiyo)

Ranar hisabi: An yiwa Saraki ihu a wurin gangamin kamfe a garin Ilori (Bidiyo)

Taron matasa da dumbin mutanen da suka halarci taron gangamin yakin neman zabe da Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya jagoranta a garin Ilori, babban birnin jihar Kwara suka yi ta yi masu ihu.

An dai ga matasan na ihu tare da fadar 'Ole' dake zaman kalmar 'barawo' da yaren Yarbanci a yayin da manyan bakin dake saman babban dandamalin yakin neman zaben ciki kuwa hadda Sanata Bukola Saraki din.

Ranar hisabi: An yiwa Saraki ihu a wurin gangamin kamfe a garin Ilori (Bidiyo)

Ranar hisabi: An yiwa Saraki ihu a wurin gangamin kamfe a garin Ilori (Bidiyo)
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Atiku Abubakar yayiwa 'yan gudun hijirar Zamfara kyautar ban mamaki

Legit.ng Hausa ta samu cewa a wani bidiyon da rika yawo a kafafen sadarwar zamani, an nuna wasu jami'an tsaro da makusantan Sanatan suna kare shi tare da manyan bakin lokacin da suke zuwa wajen motocin su.

A wani labarin kuma, gidauniyar tallafawa marasa galihu ta 'Atiku Care Foundation' ta tallafawa daruruwan 'yan gudun hijira a jahar Zamfara.

Gidauniyar tana gudanar da aikin ta tsawon lokaci wajen bada tallafin kayan abinci ga masu bukata musanman marayu masu rangwamen gata da ‘yan gudun hijira wadanda ‘yan ta’addan Boko-Haram suka raba su da gidajen su a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Ga dai bidiyon nan na matasan suna cewa 'ole':

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel