Ko me za a kira ni, sai na karbo dukiyar Gwamnati a hannun Barayi – Buhari

Ko me za a kira ni, sai na karbo dukiyar Gwamnati a hannun Barayi – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa masu sukar sa su na cewa gwamnatin sa ba ta tafiya yadda ya kamata, ba su damun sa. Ana yawan kiran shugaban kasar Baba Go Slow a Najeriya.

Ko me za a kira ni, sai na karbo dukiyar Gwamnati a hannun Barayi – Buhari
Buhari yace bai da laifi ddon a dauki lokaci ba a kai ga ci ba a harkar yaki da sata
Asali: Facebook

Buhari yace alkawuran da yake kokarin cikawa su ne wanda yayi a baya; na yaki da rashin gaskiya da inganta tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki. A cewar sa an samu nasara a fannin tattali ta hanyar noma, sannan kuma yace an samu tsaro.

A fannin yaki da barayi ne shugaban yace ake ganin rashin saurin gwamnatin sa. Shugaban kasar yace tsarin kasar ya sa ake kuka tare da hanzarin ganin an gama maganin wadanda su ka saci dukiyar al’umma, Buhari yace yana bakin kokarin sa.

KU KARANTA:

A Ranar Talatar nan ne shugaban kasar yayi wannan jawabi lokacin da ya gana da jagororin kiristoci da ke cikin Garin Abuja. Shugaba Buhari yace har gobe, ba zai kuma daina nuna wadanda su ka yi wa Najeriya illa da yatsa ba domin a san su.

Ministan birnin tarayya, Mohammed Bello yayi wa shugaban kasar addu’a na samun isasshen lafiya domin cigaba da aikin kwaran da ya soma. Haka kuma wani babban Fasto a Tawagar, Nicholas Okoh, ya ji dadin ganin yadda Buhari ya samu lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng