Sanata Wamako ya yi yayyafin kudi ga magoya bayansa, hotuna
Wasu hotuna da faifan bidiyo da suka fantsama a dandalin sada zumunta daban-daban sun nuna tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai ci, Aliyu Wamako, na watsi da kudi a gidansa ga magoya bayansa.
A jikin hotunan da faifan bidiyon, an ga Sanata Wamako na watso kudi ga jama'a daga kan benen gidansa.
Majiyar legit.ng ta shaida mata cewar lamarin ya faru ne bayan Sanatan ya je gida domin hutun kirsimeti da na karshen shekara kuma jama'a suka taru domin yi masa maraba da nuna goyon baya gare shi.
Batun watsa kudin ya jawo barkewar cece-kuce a tsakanin jama'a, inda wasu ke nuna bacin ransu da takaici bisa yadda 'yan siyasa da masu mulki suka mayar da talaka wa tamkar kaji da ake watsa wa tsaba idan ana son a kama zukatansu.
DUBA WANNAN: Faifan bidiyo: Jiki magayi, sai mun canja Buhari - Matasan Zamfara sun rera waka yayin zanga-zanga
Wamako ya kasance mataimakin gwamnan Sokoto, tsohon gwamnan jihar, sannan yanzu kuma Sanatan mai wakiltar tsakiyar jihar Sokoto.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng