Kasar India ta halatta yin luwadi da madigo

Kasar India ta halatta yin luwadi da madigo

- Kasar India ta halasta madigo da luwadi

- An yadda da hakan ne ga masu yawan shekaru

- Hakan ya dadada ran masu fafutukar son ganin yiwuwar faruwan haka

Rahotanni sun kawo cewa kotun koli a kasar India ta halasta yin luwadi da madigo a kasar, matakin da aka dade wasu na adawa da shi.

Kotun ta halatta yin hakan ne ga manya da suka mallaki shekarun girma.

Hukuncin dai ya yi wa masu gwagwarmayar kare 'yan luwadi da madigo dadi inda suka rungume juna suna murna bayan yanke hukunci da kotun tayi.

Kasar India ta halatta yin luwadi da madigo
Kasar India ta halatta yin luwadi da madigo
Asali: Getty Images

Alkalai biyar ne suka yi nazari akan hukuncin da aka yanke a shekara ta 2013.

Tsohuwar dokar tun zamanin turawan mulkin mallaka da aka fi sani da sashe na 3-7-7 ta zartar da hukuncin duk wanda aka samu da yin madigo da luwadi za a yanke masa hukuncin ko dai sama da shekara 10 a gidan kurkuku.

KU KARANTA KUMA: Shugaban Cocin Anglica: Mummunar dabi'ar Luwadi da Madigo na durkusar da ci gaban Nigeria

Tun da farko ma su fafutuka sun ce ayyana auren jinsi a matsayin laifi, zai zama babbar barazana ga 'yancin masu ra'ayin auren jinisi daya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Allah madaukakin sarki ya tona asirin wani hamshakin dan kasuwan jihar Kano da ya shahara wajen aikata luwadi da kananan Yara.

Majiyarmu ta ruwaito a ranar Laraba 25 ga watan Yuli ne wata Kotun majistri dake jihar Kano ta aika da wannan attajiri, Balarabe Habibu zuwa gidan Yari sakamakon zarginsa da ake yi da yin luwadi da wani yaro mai shekara Tara.

Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Pogu Lale ya shaida ma Kotun cewa Habibu mai shekaru 41 mazauni a unguwar Dullurawa ya aikata luwadi, wanda hakan ya saba ma sashi na 284 na kundin hukunta manyan laifuka.

Dansandan yace mahaifin wannan yaro mai suna Muratala Sa’idu tare da mahaifiyarsa Aisha Khalid ne suka kai karar wannan mutumi zuwa ofishin Yansanda dake Jakara a ranar 6 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel