Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a jihar Zamfara, an fara kone-kone

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a jihar Zamfara, an fara kone-kone

Daga zanga-zanga, rikici ya barke a jihar Zamfara kan cigaban rashin tsaro da ya hallaka daruruwan jama'a a jihar cikin shekaran nan.

Masu zanga-zangan a karamar hukumar Tsafe da ke jihar da safiyar ranan Litinin sun tare babban hanyar Gusau zuwa Zaria da ake bi zuwa jihar Kaduna, Kano da Abuja.

Wani idon shaida ya bayyanawa manema labarai cewa yan zanga-zangan sun lalata hotunan yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar, AbdulAziz Yari.

Daga lokacin aka fara samu sabani har ya kai ga fadace-fadace tsakanin masu zanga-zanga.

Wan majiya mai karfi ya bayyana cewa: "Yan zanga-zangan sun tare hanya kuma suna kona tayoyi, a yanzu haka, sun kona sakatariya karamar hukumar tsafe."

KU KARANTA: Ana saura makonni uku aurensa ya rasu

Mun kawo muku rahoton cewa an hallaka akalla mutane 40 a cikin mako biyu kacal a yankin karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

Yan fashi dai sun addabi al'umman Zamfara da yawan hare-hare duk da matakan da hukumomin tsaron Najeriya ke cewa suna dauka da nufin murkushe su.

A yammacin Asabar sai da suka hallaka akalla mutane 16 a kauyen Magamin Diddi na karamar hukumar Muradun da ke jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel