Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin sabunta dokar hukumar NBC, ya bayyana daili

Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin sabunta dokar hukumar NBC, ya bayyana daili

- Dr Bukola Saraki ya karanta wata wasika da Buhari ya aikewa majalisar, inda ya sanar da su kin amincewarsa na sa hannu a kudirin sabunta dokar hukumar NBC

- A cikin wasikar, shugaban kasar ya bayyana cewa kin sa hannunsa kan dokar ya faru ne sakamakon cire wani iko na hukumar da aka yi na sakin layi na 21(U)

- Buhari ya shawarci majalisar dattijan da ta sake yin gyara kan wannan kudurin sabunta dokar, tare da basu tabbacin sa hannu kan dokar da zaran ya gamsu da gyaran

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da sa hannu a wani kuduri da aka gabatar masa na son sabunta dokar da ta kafa hukumar kula da kafofin watsa labarai ta kasa NBC.

A baya bayan nan ne majalisar tarayya ta aikewa Buhari kudirin sabunta dokar don tabbatar da ita a matsayin dokar da aka sabunta wacce ke kula da harkokokin hukumar NBBC, da ke sa ido kan kafofin watsa labarai na kasar.

Mr Buhari ya bayyana wannan kin amincewa nasa na sa hannu kan kudurin sabunta dokar a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki.

Mr Saraki ya karanta wanna wasika a zaman da majalisar dattijan ta gudanar a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Ana wata ga wata: Jami'ar ABU ta bi sahun SSANU na shiga yajin aiki

Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin sabunta dokar hukumar NBC, ya bayyana daili

Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin sabunta dokar hukumar NBC, ya bayyana daili
Source: Twitter

A cikin wasikar, shugaban kasar ya bayyana cewa kin sa hannunsa kan dokar ya faru ne sakamakon cire wani iko na hukumar da aka yi na sakin layi na 21(U) da ke cikin kudurin da majalisar ta gabatar masa, wanda kuma wannan sakin layin na 21(U) na kunshe da wasu muhimman iko da aka baiwa hukumar wanda rashin zai kiya kawo cikas ga gudanarwar aikinta.

"La'akari da sashe na 58(4) na kundin dokar kasar Nigeria kamar yadda aka sabunta, Ina so in sanar da majalisar dattijai cewa, na yanke shawara a ranar 26 ga watan Nuwamba 2018, ba zan sa hannu akan sabunta dokar hukumar NBC zuwa doka ta 2018 ba.

"Na yanke wannan hukunci na kin sa hannu kan kudirin sabunta dokar ne saboda wani sashe na musamman da aka cire daga cikin ainihin dokar da ta kafa hukumar, sakin layi na 21(U) na dauke da muhimman iko da hukumar ke tafiyar da ayyukanta da shi, rashin wannan iko zai gurguntar da gudanarwar hukumar.

"Ina bayar da shawarar sake yin anzari kan wannan kudurin sabunta dokar da aka gabatarmun, musamman ma na maido da sakin layi na (U), idan ya so sai a sake sanyawa sakin layin na yanzu wani suna da daban, ko zuwa sakin layi na (Y).

"Ina fatan shugaban majalisar, zaka amince da wannan shawarar, da kuma baka tabbacin damar sake duba kudurin dokar idan aka yi gyara akanta," cewar wasikar da shugaban kasa Buhari ya aikewa majaloisar dattijan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel