Zargin kudi: CAN ta gudanar da bincike na musamman kan babban Shugaban ta

Zargin kudi: CAN ta gudanar da bincike na musamman kan babban Shugaban ta

Mun samu labari cewa babban kwamitin Kungiyar CAN ta kiristocin Najeriya ta rushe Majalisar Dattawan ta bayan wani bincike da uwar Kungiyar ta Mabiya addinin Kirista ta gudanar kwanan nan.

Zargin kudi: CAN ta gudanar da bincike na musamman kan babban Shugaban ta
Dattawan CAN sun zargi Ayokunle da karbar kudi daga Gwamnati
Asali: Facebook

Kwanakin baya ne Dattawan Kungiyar ta CAN su kayi wani rubutu inda su ka zargi shugabannin Kiristocin Kasar da karbar makudan kudi har Naira Miliyan 40 a matsayin kudin mota bayan sun kai wa Shugaban kasa Buhari ziyara.

Wani kwamiti da aka nada tayi bincike game da zargin da ke wuyan shugabannin Kungiyar ta kammala aiki ta gano cewa ba su da laifi kamar yadda Dattawan na CAN su ke ikirari. Kwamitin ya maida raddi ne ga ‘Ya ‘yan na sa a Jarida.

KU KARANTA: Boko Haram: Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi Kasashen Duniya

A jawabin da kwamitin ya fitar, ya bayyana cewa rade-radin da ke yawo na cewa shugaban Kungiyar CAN da wasu, sun karbi kudi a hannun Shugaban kasa ba gaskiya bane. Kwamitin ya kuma ja kunnen masu yada wannan jita-jita.

Haka zalika wannan kwamiti ya tabbatar da cewa an yi wannan ne domin batawa shugaban Kungiyar suna kuma bayan an yi dogon bincike an gano cewa sharri ne kurum aka kitsa da kage saboda wasu dalilai na neman Duniya.

Kwamitin ya kara da cewa wanda ya fara wannan zargi, ya ki zuwa gaban su domin ya kare kan sa duk da. CAN dai yanzu tayi watsi da wannan kungiya da ta ce ta na jin haushin yadda ake gudanar da sha’ani ne babu hannun ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel