A mako mai zuwa ASUU za ta fitar da matsaya game da yajin aiki – Ogunyemi

A mako mai zuwa ASUU za ta fitar da matsaya game da yajin aiki – Ogunyemi

A wani dogon zama da aka yi tsakanin Malaman Jami’o’in Najeriya da kuma Gwamnatin Tarayya, an gaza cin ma matsaya inda za a cigaba da yajin aiki a Kasar. Yanzu za a kuma wani zaman a Ranar Litinin.

A mako mai zuwa ASUU za ta fitar da matsaya game da yajin aiki – Ogunyemi
Zaman ASUU da Malaman Jami’a bai haifar da ‘Dan mai ido ba
Asali: UGC

Kungiyar ASUU ta gana da Gwamnatin Najeriya a karo na 5 a cikin kusan watanni 2 da aka yi ana yajin aiki. Zaman da aka yi jiya a Birnin Tarayya Abuja na kusan sa’a 6 bai sa an yi cin ma wata matsaya ba, don haka ne aka tashi baran-baran.

Kamar yadda mu ka samu labari, ba a cin ma matsaya tsakanin Gwamnatin Tarayya da Malaman Jami’o’in kasar ba. Ministan kwadago, Chris Ngige, wanda yanzu yake jan ragamar tattaunawar yace za a sake wani zama a Ranar 17 ga Wata.

Ministan kwadagon ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa har yanzu Gwamnati ta gaza cika duka alkawuran da ta dauka a 2017. Dr. Ngige yace Gwamnati za ta sake duba lamarin albashin Ma’aikatan na Jami’o’i kamar yadda su ka yi alkawari can.

KU KARANTA: Yajin aiki: Abubuwa sun sukurkucewa Daliban Jami’oin Najeriya

Ngige yace inda ake samun matsala shi ne wajen sakin makudan kudin da aka yi alkawari domin inganta harkar ilmi a Kasar, Ministan yace karancin kudin shiga ne ya hana Gwamnatin Kasar cika wannan alkawari da ta dauka a baya.

Dr. Chris Ngige ya kuma tabbatar da cewa za a duba lamarin alawus din Ma’aikatan tare da kuma zama game da abin da ya shafi Jami’o’in Jihohi. Ngige yace Gwamnatin Kasar ta damu da wannan yajin aiki da aka yi har tsawon makonni 5 ana yi.

Shugaban Kungiyar ASUU, Biodun Ogunyemi, ya bayyana cewa za su jira har zuwa zaman d za ayi a Ranar Litinin domin sanin cewa ko za su janye yajin aikin ko kuma za su zarce. ASUU dai za ta jira ne ta ga irin kamun ludayin Gwamnatin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng