‘Yan Sanda sun kama wasu Matasa 6 su na keta hotunan ‘Yan takara a Legas

‘Yan Sanda sun kama wasu Matasa 6 su na keta hotunan ‘Yan takara a Legas

- Wasu masu lika fastocin Yele Sowore sun shiga hannun ‘Yan Sanda

- An kama wadannan Matasa ne su na kokarin keta cire fastocin wasu

- Jami’an ‘Yan Sanda za su maka su a gaban Kotu domin ayi shari’a

‘Yan Sanda sun kama wasu Matasa 6 su na keta hotunan ‘Yan takara a Legas
Kwamishinan 'Yan Sanda Edgal Imohimi na Jihar Legas a ofishin sa
Asali: Depositphotos

Jami’an Yan Sandan Najeriya da ke Garin Legas sun yi ram da wasu Bayin Allah da ke kokarin lika fastocin ‘Dan takarar Jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, cikin duhun dare. Jami’an tsaro sun ce wannan aiki ya sabawa dokar Jihar.

Jami’in da ke magana da yawun bakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas, CSP Chike Oti, ya bayyana cewa doka ta haramta manna fastocin ‘Yan takara a cikin tsakar dare. A cikin Jihar Legas ana lika fastocin zabe ne da rana tsaka.

Chike Oti, da yake bayyana dalilin yin ram da wadannan mutane da aka yi, yace aikin da su ka yi, ya sabawa yarjejeniyar da ’Yan siyasa su ka shiga a gaban Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Legas, CP Edgal Imohimi, kwanakin baya.

KU KARANTA: Yarbawa za su karbe mulki a 2023 idan Inyamurai su ka yi wasa - Ngige

Rundunar Jami’an tsaro na musamman ne su ka kama wadannan mutane har 6 da kimanin karfe 2:30 na tsakar dace. ‘Yan Sandan sun bada sunan wadanda aka kama kamar haka: Olagokun Odunayo, Michael Kate Ugaju Joseph.

Jami’an tsaron sun samu wadannan Matasa su na keta fastocin wasu ‘Yan takaran, sannan su na lika hotunan Omoyele Sowore na Jam’iyyar adawar AAC a kan titunan da ke cikin Unguwar GRA da ke Garin Ikeja da safiyar Ranar Lahadi.

Sauran wadanda aka kama sun hada da Damilola Omidiji, Banwo Olagokun da kuma Kool-Kloud Henry. Yanzu dai ‘Yan Sandan na Najeriya sun tabbatar da cewa za su maka wadannan Samari har su 6 a gaban Kotu domin a hukunta su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel