Mu leka kotu: An garkame wani dan aikin gida bayan satar sarkar N300,000 mallakin matar gida

Mu leka kotu: An garkame wani dan aikin gida bayan satar sarkar N300,000 mallakin matar gida

- Wata kotu ta bayar da umurnin cewa, a garkame wani dan aikin gida mai suna Isiaka Usman, a gidan kurkuku, wanda a ke zaginsa da satar sarkar gwal, da kudinta ya kai N300,000

- Rundunar 'yan sanda na tuhumar Usman da laifin sata.

- Emmanuel ya dage sauraron karar har sai 21 ga watan Disamba, sai dai, Usman ya ce sam bai aikata wannan laifi da ake zarginsa ba

Wata babbar kotun al'adu da ke zama a Kaduna, a ranar Laraba, ta bayar da umurnin cewa, a garkame wata 'yar aikin gida mai suna Isiaka Usman, mai shekaru 25 a gidan kurkuku, wanda rundunar 'yan sanda ke zaginsa da satar sarkar gwal, da kudinta ya kai N300,000.

Rundunar 'yan sanda na tuhumar Usman da laifin sata.

Alkalin kotun, Mr Ibrahim Emmanuel, ya bayar da wannan umurnin, bayan da jami'in shigar da karar, Sifeta Chidi Leo, ya bukaci kotun a baki, da ta tsare Usman a gidan kurkuku, kasancewar basu kammala bincike akansa ba.

KARANTA WANNAN: Rundunar sojin Najeriya na bukatar N9bn don siyan takalman sojoji a duk shekara

Mu leka kotu: An garkame wani dan aikin gida bayan satar sarkar N300,000 mallakin matar gida
Mu leka kotu: An garkame wani dan aikin gida bayan satar sarkar N300,000 mallakin matar gida
Asali: UGC

Emmanuel ya dage sauraron karar har sai 21 ga watan Disamba.

Tun farko, Leo ya shaidawa kotun cvewa wanda ake karar ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Nuwamba da misalin karfe 2 na rana a yankin Ali Akilu da ke jihar Kaduna.

Leo ya ce wanda ake zargin, da ke aikiwa Mohammed Sani, mazaunin titin Ali Akilu a Kaduna, ya saci sarkin gwal da darajarta yakai N300,000.

Ya ce wanda ake zargin, a ranar 22 ga watan Nuwamba, ya shiga dakin mai gidan tare da sace sarkar kwal daga cikin durowar sanya kayansa.

Wanda ya shigar da karar ya ce laifin ya ci karo da sashe na 390 da 427 na dokar aikata laifuka ta jihar Kaduna ta 2017.

Sai dai wanda ake zargin ya ce sam bai aikata wannan laifi da ake zarginsa ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel