Hukumar JAMB ta karyata rade-radin fara saida fam din jarrabawar UTME

Hukumar JAMB ta karyata rade-radin fara saida fam din jarrabawar UTME

Mun ji cewa Hukumar JAMB da ke gudanar da jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare a Najeriya ta musanya rahotannin da ake ta yadawa na cewa an soma saida fam din jarrabawar 2019.

Hukumar JAMB ta karyata rade-radin fara saida fam din jarrabawar UTME
Daga Watan Junairu za a soma rajistar jarrabawar UTME
Asali: UGC

Hukumar ta JAMB ta karyata wannan rade-radi da ke yawo ne ta bakin Fabian Benjamin wanda shi ne ke magana a madadin ta. Benjamin ya fadawa Jaridar Premium Times cewa ba a fara saida jarrabawar shekarar badi ba tukun.

Mista Fabian Benjamin ya bayyana cewa za a fara saida fam din jarrabawar UTME watau ‘Unified Tertiary Matriculation Examination’ da ake yi domin shiga makarantun gaba da sakandare ne a farkon shekara mai zuwa na 2019.

KU KARANTA: Makauniyar da ta kammala karatun shari’a ta gana da Gwamnan Kaduna

A wannan shekarar, Hukumar ta JAMB ta soke tsarin da ta saba na fara rajistar jarrabawar UTME tun a karshen shekara. Hakan ya zo ne bayan rage kudin jarrabawar da Gwamnatin Tarayya tayi kwanan nan inji Kakakin Hukumar kasar.

Har wa yau, Hukumar jarrabawar tace za ta bada makonni 6 ne rak na yin rajista domin rubuta jarrabawar ta UTME. An kuma ja-kunnen masu zana wannan jarabawa da su bi a hankali, kar su fada hannun miyagun ‘yan damfara.

Idan ba ku manta ba, Ministan ilmi Malam Adamu Adamu ya tabbatar da cewa an rage kudin jarrabawar NECO zuwa N9850 yayin da jarrabawar BECE ta koma BECE. Za kuma a rika biyan N3500 ne kafin a rubuta jarrabawar UTME a badi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng