Harin Buni Gari : Gawarwakin Soji 2 sun sake bayyana a jihar Yobe

Harin Buni Gari : Gawarwakin Soji 2 sun sake bayyana a jihar Yobe

Kamar yadda wata majiyar rahoto ta bayyana a jiya Litinin, shafin jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, an sake tsinto gawarwakin wasu Soji biyu cikin dokar Daji bayan aukuwar harin kungiyar ta'adda ta Boko Haram kan sansanin dakaru da ke yankin Buni Gari na jihar Yobe a ranar Asabar din da ta gabata.

Majiyar rahoton yayin bayyana ruwayoyinta a jiya Litinin ta kuma bayyana cewa, kawowa yanzu akwai dakarun soji da aka nema kuma aka rasa bayan bayan aukuwar wannan mummunan hari na bazata.

Majiyar shafin na jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an mika gawarwakin sojin biyu zuwa dakin killace Gawa na babban Asibitin garin Damaturu da adadin gawarwakin Soji ya kasance takwas a halin yanzu.

Harin Buni Gari : Gawarwakin Soji 2 sun sake bayyana a jihar Yobe

Harin Buni Gari : Gawarwakin Soji 2 sun sake bayyana a jihar Yobe
Source: Twitter

Rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa ya bayyana cewa, kawowa yanzu ba bu wani furuci ko sanarwa daga banagaren hukumar sojin kasar nan dangane da wannan mummunan hari da ya auku a karshen makon da ya shude.

KARANTA KUMA: Zan bayar da tallafi ga Manoman da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a bana - Buhari

Ko shakka ba bu wani babban jami'in sojin kasa, Birgediya Janar Muhammad Baba Dala, ya ziyarci Asibitin na garin Damaturu domin ganewa idanunsa tare da kwasar rahoto tun daga mafararsa da kuma tushe.

Kazalika jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani tsohon sojan kasa na Najeriya, Janar John Gbor, ya fito takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APGA inda zai fafata yayin babban zabe na 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel