Rashin sa'ar samun masu gida, wasu 'yan fashi da makami sun bar sakon suna nan dawowa

Rashin sa'ar samun masu gida, wasu 'yan fashi da makami sun bar sakon suna nan dawowa

Cikin wani rahoto da muka samu da sanadin shafin jaridar Sahara Reporters ya bayyana cewa, a sakamakon fushi da bakin ciki na rashin samun masu gida, ya sanya wasu 'yan Fashi da Makami sun bar sakon cewa suna nan dawowa.

Wannan lamari da ko shakka ba bu ya auku ne cikin wani gida a yankin Iyese da ke karkashin karamar hukumar Ado Ota ta jihar Ogun a ranar Asabar ta makon da ya shude.

'Yan ta'addan masu Fashi da makami kamar yadda rahotanni suka bayyana sun yi iyaka bakin kokarin su na yashe duk wata dukiya da ke cikin wannan gida amma rashin samun masu gida ya sanya kasuwarsu ba tayi riba ba.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, Miyagun da suka ketare iyakar wannan gida ta saman rufin kwano inda yayin duk wani yunkuri hakarsu ba ta cimma ruwa ba sakamakon murafen kofofin gidan da suka taras a garkame.

Rashin sa'ar samun masu gida, wasu 'yan fashi da makami sun bar sakon suna nan dawowa
Rashin sa'ar samun masu gida, wasu 'yan fashi da makami sun bar sakon suna nan dawowa
Asali: Facebook

Cikin fushi gami da bakin cikin rashin samun nasara wajen balle murafen kofofin ya sanya suka harzuka wajen barin rubutaccen sako ga mamallakan wannan gida kan cewa suna nan dawowa tare da neman sa'a da shan alwashi.

Sakon cikin harshen turanci a wata rubutacciyar takarda da manema labarai suka samu damar hangawa ya bayyana kamar haka; "We are Coming back o !!! Goodluck."

KARANTA KUMA: Rayuka 4 sun salwanta, Mutane 8 sun jikkata a wani Hatsari da ya auku a jihar Nasarawa

A yayin da wannan korafi ya kai ga ofishin 'yan sanda reshen katafariyar gona ta Ota Farms mallakin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, babban jami'in dan sanda na reshen ya bayar da umarnin fantsamawa cikin bincike domin taso keyar wannan Mazalunta.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kungiyar Matasan nan ta garin Yauri na jihar Kebbi da suka dugunzuma wajen kidayar buhun hatsi na Gero, sun kammala kidayarsu bayan watanni shida, inda suka tabbatar da adadin kwarori 11, 979,868 cikin Buhun Gero guda.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel