APC ta kayar da PDP a zaben maye a jihohin arewa 3

APC ta kayar da PDP a zaben maye a jihohin arewa 3

'Yan takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC ne INEC ta bayyana cewar sun yi nasara a zaben maye gurbi da aka yi a jihohin Bauchi, Katsina, da Kwara.

An gudanar da zabukan maye wasu kujeru daban-daban a jihohin 3.

A jihar Katsina, Abubakar Kusada na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben maye na mazabar Kankia/Kusada/Ingawa.

Kusada ya samu kuri'u 48,518, fiye da na dan takarar da ke biye ma sa, Abdulssamad Yusuf na jam'iyyar PDP.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Rasheed Adebayo, baturen hukumar zabe, ya sanar da cewar Kusada ne ya lashe zaben bayan samun kuri'u ma fi rinjaye.

Yusuf Nuhu, dan takarar jam'iyyar APC, ne ya lashe zaben maye gurbin kujerar dan majalisar wakilai na mazabar Toro a jihar Bauchi.

Dan takarar na APC, Yusuf Nuhu, ya samu kuri'u 22,317 yayin da Shehu Buba na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 18,235.

APC ta kayar da PDP a zaben maye a jihohin arewa 3
APC ta kayar da PDP a zaben maye a jihohin arewa 3
Asali: Depositphotos

Nuhu ya samu nasara a mazabu 11, yayin da Buba ya lashe mazabu 3 kacal.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Ahmad Tijjani Fagam, ya ce dan takarar jam'iyyar APC ne ya lashe zaben saboda ya samu kuri'u ma fi rinjaye.

A daren jiya, Asabar, ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta yi nasarar lashe zaben maye gurbi na kujerar majalisar wakilai ta mazabar Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero.

DUBA WANNAN: Babu adalci da sanin ya kamata a PDP - Gwamnan jam'iyyar

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Abimbola Adesoji, baturen zabe na hukumar INEC, ya bayyana cewar APC ta samu kuri'u 21,236 yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 18,095.

Ya kara da cewar Labour party ta samu kuri'u 150, jam'iyyar PPN ta samu kuri'u 76, sai kuma jam'iyyar UPN da ta samu kuri'u 42.

Farfesa Adesoji ya ce an kada jimillar kuri'u 40,930 a zaben, adadin kuri'u 1,331 ne su ka lalace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel