Dogara dan siyasa ne mara karfi a Bauchi – Gwamna Abubakar
Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya bayyana cewa ya yi imani da cewar jam’iyyar sa ta All Progressives Congress (APC) ta fi babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) kaifi wajen nasara.
A wani hira da manema labarai, gwamnan ya ce kamfen da za’a fara zai bayar da damar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar za su gabatar da nasarorinsu a wajen yan Najeriya.
Gwamnan ya kuma yi Magana kan sauran lamura ciki harda zaben fidda gwani na APC, ma’aunin siyasar Yakubu Dogara a Bauchi da kuma nasarorinsa.

Asali: Depositphotos
A cewarsa siyasa ta gaji rikicin cikin gida, sai dai akan san karfin jam’iyya ne wajen iya shawo kan matsalolinta sannan ta magance su.
Yace babu shakka jam’iyyar PDP ta yi zaben fidda gwani na shugaban kasa cikin nasara, sai dai duk sauran zabukan fidda gwanin da suka biyo baya sun tayar da kura.
KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama manyan yan fashi 4 a Abuja
Ya kuma bayyana cewa kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara bai da karfi a jihar Bauchi, domin a cewar gwamnan da suka fara yan majalisar wakilai uku ne kadai ke tare da shi amma a yanzu yan majalisa tara cikin 12 suna tare das hi.’
Ya ce kuma maganar gaskiya zuciyar Dogara ba tare da APC domin a cewarsa anyi duk kokarin ganin an taushe shi amma sai da ya sauya sheka.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng