Wata babbar kotu ta daure wani kasurgumin dan luwadi a wata jihar Arewa

Wata babbar kotu ta daure wani kasurgumin dan luwadi a wata jihar Arewa

Kotu dake Tunfure jihar Gombe ta daure wani magidanci mai suna Zakariya Shehu da ta kama da laifin yin lalata da dan shekara 12 ta dubura.

Lauyan da ya shigar da karar Kabiru Shuaibu ya bayyana wa kotu cewa Shehu mai shekar 29, mazaunin kwatas din Jekadafari ne a garin Gombe sannan ya aikata wannan ta’asa ne a watan Satumba.

Wata babbar kotu ta daure wani kasurgumin dan luwadi a wata jihar Arewa

Wata babbar kotu ta daure wani kasurgumin dan luwadi a wata jihar Arewa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Yadda ake wanke dakin Ka'abah

Ya ce Shehu ya danne wannan yaro ne a dakin ajiye kaya a Tashar Dukku dake garin Gombe .

Shuaibu ya nemi alfarmar kotun data daga shari’ar wannan kara domin jami’an tsaro su kammala bincike.

Alkalin kotun Japhet Maida ya daga shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba sannan ya bada umurin a tsare Shehu a hannu ‘yan sanda har sai an kammala shari’ar.

A wani labarin kuma, Wani ma'aikaci da gidan yada labarai na Rediyo da Talabijin a jihar Kaduna na DITV-Alheri mallakar tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasa aikin sa sakamakon nuna soyayyar shugaba Buhari karara a dandalin sadarwar zamani.

Majiyar mu ta Daily Nigerian ta ruwaito mana cewa shi mai kafar sadarwar zamanin, Mista Baba-Ahmed tsohon na hannun damar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da yayi masa dan sa ido a zaben shekarar 2019 a jam'iyyar APC kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel