Dubu ta cika: Wani barawon mota dake basaja a matsayin Soja ya shiga hannu
Rundunar Yansandan jahar Ondo ta samu nasarar damke wani matashi dake sanya kayan Sojoji yana basaja bayan ya saci wata babbar motar alfarma Jeep, kiraa Toyota Sequila a garin Ondo, inji rahoton jaridar Punch.
Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, Femi Joseph ne ya sanar da haka a ranar Laraba 17 ga watan Oktoba, inda yace wannan Sojan gona da aka kama da laifin sata ya bayyana sunansa da Abubakar Aliu.
KU KARANTA: Abin nema ya samu: Kotu ta baiwa EFCC izinin rike Fayose na tsawon kwanaki 14
Kaakakin yace Aliu ya saci motar ne mai lamba AGL 230 EH, a wani gajerin gyaran motoci a garin Ondo, inda ya yi gaba da motar zuwa jahar Kogi, inda a can ne dubunsa ta cika bayan Yansanda sun bi sawunsa, suka kama shi.
“A ranar 5 ga watan Oktoba aka kai rahoton sace wannan mota a ofishin Yansanda dake Enu-Owa a garin Ondo, masu karar sun ce Abubakar Aliyu ya bayyana musu shi Soja ne, kuma sunansa Kanal Faruk Aliyu, a lokacin da ya isa garejin motar da wata mota kirar Pijo 406 don a gyara masa.
“Shigarsa garejin ke da wuya, sai ya hangi wata motar Toyota Sequila Jeep ta sayarwa, sa’annan ya nuna sha’awar sayan motar, aka yi ciniki aka sallama masa akan kudi naira miliyan 1 dubu 200.
“Daga nan sai ya dauki motar don ya gwadata ya ji lafiyarta, daga fitarsa bai kara dawowa ba har sai ranar Yansanda suka bi sawunsa zuwa garo Gegu Beki dake jahar Kogi, inda aka kama shi.” Inji Kaakaki.
A wani labarin kuma, rundunar yansanda ta musamman dake karkashin ikon babban sufetan Yansanda sun samu nasarar kama wasu mutane sha uku dake cinikin jarirai tare da safarar mutane a jahar Kogi, daga cikinsu har da wasu ma’aurata da suka sayar da jaririnsu akan kudi N250,000.
Ku biyo mu a https://facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng