Daidai ruwa daidai tsaki: Kalli irin kyautan da samari ke siya ma yan matansu a ranar masoya

Daidai ruwa daidai tsaki: Kalli irin kyautan da samari ke siya ma yan matansu a ranar masoya

An hangi wasu samari su biyu suna kokarin tsintar ma yan matansu rigar mama a kasuwar gwanjo, wanda alamu sun nuna wadannan rigunan maman zasu baiwa yan matansu.

daidai ruwa daidai tsaki: Kalli irin kyautan da samari ke siya ma yan matansu a ranar masoya
daidai ruwa daidai tsaki: Kalli irin kyautan da samari ke siya ma yan matansu a ranar masoya

Idan dai mai karatu bai manta ba a yau ne ake yin bikin ranar masoya ta duniya, wato Valentine a Turance, jama’a a yanar gizo suna ganin samarin zasu mika yan matan rigunan maman ne a matsayin kyauta don tabbatar musu soyayyar da suke yi musu.

KU KARANTA: Matasan Musulmai sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da ranar masoya

Abinka da dan Najeriya barkanci, hakan ya janyo cece kuce da tsokane tsokane tsakanin samari da yan mata.

Sai dai, wasu ma’abota kafafen sadarwa na ganin ai daidai ruwa daidai tsaki, ma’ana samarin sun yi iya abinda karfinsu zai iya ne, ganin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel