Malaman addinin kirista sun shirya addu’ar kwana 40 don nema ma Buhari nasara a 2019
Wasu malaman addinin kirista daga kungiyoyi daban daban sun kaddamar da addu’ar kwanaki arba’in don nema ma shugaban kasa Muhammadu Buhari nasara a kokarinsa na neman tazarce akan mulkin Najeriya a yayin zaben shekarar 2019.
Malaman sun fito ne a karkashin lemar hadaka ta National inter-faith and Religious Organisation for peace (NIFROP) a jahar Filato, inda suka shirya wata addu’ar ta daban ta neman dawamammen zaman lafiya mai daurewa a kasar Najeriya.
KU KARANTA: An fallasa wani gwamna daga yankin Arewa da aka kama yana karbar cin hancin dala miliyan 5
A cikin wata sanarwar da jagoran addu’ar, Sunday Garuba ya fitar, yace Allah ne ya turo Buhari domin ya ceto Najeriya daga rushewar da ta kusa yi, don haka yace Allah sai ya karya duk wasu makiyan Najeriya, na fili da na boye.
“Ana gab da gudanar da zaben 2019, don haka duba da kyawawan ayyukan da shugaba Muhammadu Buhari ke gudanarwa, mun kaddamar da addu’ar kwanaki 40 mai taken ‘Buhari zai dawo a 2019’, musamman a yanzu da makiyan Najeriya suka fara shirya tuggu iri iri don ganin sun mayar da kasar baya.
“Amma da ikon Allah, hakarsa ba za ta cimma ruwa ba…………….zamu fara taron addu’ar da yabo ga Ubangijinmu ta hanyar wake wake, daga nan kuma zamu dukufa addu’a ga Najeriya, addu’a ga shugaba Buhari, addu’a ga ministocinsa, addu’a ga Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram, addu’a game da zaben dake karatowa, sai kuma addu’ar samun nasarar Buhari a zabukan.” Inji Garuba.
Daga karshe Faston yace zasu gudanar da addu’ar godiya ga Allah da ya baiwa Najeriya nasara akan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram har ta kai ga yanzu an karyasu, da nasarar karya yan siyasa makiyan Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa
Asali: Legit.ng