2019: Shugaba Buhari ya saki zafafan hotunan yakin zabe
A ranar Asabar ne wakilai, shugabanni da masu ruwa da tsaki a tafiyar da jam'iyyar APC mai mulki suka tattara a Abuja domin tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa bayan nasarar da ya samu a zaben fitar da dan takara da aka gudanar a fadin Najeriya.
Da yake sanar da sakamakon zaben, zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, wanda shine shugaban kwamitin taron, ya bayyana cewar a kalla daliget 7,000 daga fadin jihohin Najeriya 36 ne suka tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takarar APC.
DUBA WANNAN: 2019: Obasanjo ya saki sabon sako a kan nasasarar Atiku a zaben PDP
Bayan kaddamar da takaran ne sai wasu hotunan shugaba Buhari cikin kayan manyan kabilun kasar nan suka bullo a yanar gizo. Hotunan sun samo asali ne daga wasu hadiman shugaba Buhari da suka sa hotunan a shafukansu na yanar gizo.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng