Zaben Fidda Gwani: Wakilan Jam'iyyar PDP sun raba Gari tsakanin Tambuwal da Bafarawa

Zaben Fidda Gwani: Wakilan Jam'iyyar PDP sun raba Gari tsakanin Tambuwal da Bafarawa

Mun samu cewa wakilan jam'iyyar PDP daga sassa daban-daban na fadin kasar nan na ci gaba da tururuwa zuwa birnin Fatakwal na jihar Ribas, inda za a gudanar da gangamin jam'iyyar domin fidda gwanin takarar kujerar shugaban kasa.

A yayin wannan lamari tsama tayi kane-kane tsakanin wakilan jam'iyyar reshen jihar Sakkawato dangane da manema takarar kujerar guda biyu kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana.

Manema takarar biyu sun hadar da tsohon gwamnan jihar Sakkawato, Attahiru Bafarawa da kuma gwamna mai ci a jihar a halin yanzu, Aminu Waziri Tambuwal da suke cikin mutane 13 masu hankoron tikitin takara na jam'iyyar.

Zaben Fidda Gwani: Wakilan Jam'iyyar PDP sun raba Gari tsakanin Tambuwal da Bafarawa
Zaben Fidda Gwani: Wakilan Jam'iyyar PDP sun raba Gari tsakanin Tambuwal da Bafarawa
Asali: UGC

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, manema takarar biyu sun bayyana ra'ayin da sanadin hadimansu kan cewa ba bu gudu ba bu ja daya dangane da wannan lamari sai dai kowa ta tashi ta fisshe shi kuma wanda ya iya Allonsa ya wanke.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Wata Mata ta Haifi 'Yan 3 duka Maza a jihar Kano

A yayin da ake tuntube-tuntube na yiwuwar kulla yarjejeniya tsakanin manema takarar biyu domin daya ya janyewa daya, kowanen su ya nuna rashin yiwuwar hakan da cewar a bari ya huce shi ke sanyawa a ci da rabon wani.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, zaben fidda gwanin takarar gwamna ya bar baya da kura a jihohin Yobe da Abia inda wadanda suka sha kashi yayin zaben ke bayyana rashin amincewar su kan sakamakon zaben.

Na nan tafe: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel