An rataye budurwa a kasar Iran, bayan da ta kashe mijin da ke cuzguna mata

An rataye budurwa a kasar Iran, bayan da ta kashe mijin da ke cuzguna mata

- An kashe ta bayan da tace shi da kaninsa ke mata fyade

- An mata auren dole ne tana da shekaru 15

- Amnesty International ta koka da kisan

An rataye budurwa a kasar Iran, bayan da ta kashe mijin da ke cuzguna mata
An rataye budurwa a kasar Iran, bayan da ta kashe mijin da ke cuzguna mata
Asali: Twitter

Kungiyoyin kare hakkokin yara da mata, sunyi tir da Allah-wadai da rataye wata kyakkyawar budurwa 'yar asalin kabilar Kurdawa dake Iran, mai shekaru 24, bayan da ta shafe shekaru a kulle saboda laifin kashe mijinta da wuka.

A baya dai, ta amsa laifin, inda tace dashi da qaninsa suna yi mata fyade ta dole ne, a aure da aka yi mata tana da shekaru 15 da haihuwa.

A kasar Iran dai ana aiki ne da shari'ar Islama, wadda tace mace na balaga ne daga fara haila, maimakon kimiyyar da tace hankali ke fadin balaga, a shekarun 18-21.

DUBA WANNAN: ASUU ta gano kitimurmurar kara kudin makaranta

An dai yi ta kaje-kazo kan kokarin kare hakkinta a matsayin karamar yariinyar da aka yi wa auren dole, amma shuwagabannin Iran din suka yi kememe suka ce sai anyi mata hukunci daidai da laifinta, duk da ta janye shaidar da ta bayar, inda tace ta dole aka mata tace ita tayi kisan.

Ta bayyana cewa mijin, ya mutu ne ta hanyar caka wuka, kuma dan'uwan nasa ne yayi kisan.

Shidai dan uwan nasa, ya muusanta yi mata fyade, kuma yace in ta amsa cewa ita tayi kisan, to zai yafe mata, abu da tace sam baza ta amsa ba, tunda ba ita tayi ba.

Idan da ta amsa din, yana iya yafe mata, wanda a shariance, sai kotu ta sake ta, tunda shi danuwansa ne, to amma kuma watakil yaki yafewar koda ta ce ita tayi, tunda shima akwai yiwuwar ta shigar da kara kan fyaden da tace yayi mata bilaa-adadin.

Yanzu dai, Zeinab Sekaanvand, ta mutu jiya a kurkuku ta hanyar rataya, kuma ta sha azaba a kulle tun daga 2012 zuwa jiya, ta dai huta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel