Fallasa: An gano ashe Ambode ya kebe da alkalan zabe don neman wata alfarma

Fallasa: An gano ashe Ambode ya kebe da alkalan zabe don neman wata alfarma

Wata majiya ta sanar da The Cable cewar gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Legas ya yi wata ganawar sirri da mambobin kwamitin gudanar da zaben cikin gida na jam'iyyar APC da aka tura Legas domin su gudanar da zaben a ranar Litinin.

Majiyar ta ce 'yan kwamitin karkashin jagorancin Clement Ebri sun tsaya a dakin Otel dinsu har zuwa karfe 1 na ranar Talata yayin da ake gudanar da zabuka a mazabu 245 da ke Legas inda sakamakon zabukan ke nuna Jide Sanwo-Olu ne ke samun rinjaye.

Sai dai daga baya Kwamitin ta fito ta soke zaben da aka fara gudanarwa inda ta ce za'a sake sabuwar zabe.

Ta Tonu: Yadda Ambode ya kebe da alkalan zabe don neman hadin kansu
Ta Tonu: Yadda Ambode ya kebe da alkalan zabe don neman hadin kansu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Amsar da Buhari ya bawa wata kasa da ta nemi taimakon Najeriya wajen warware matsalolin ta

Majiyar Legit.ng ta gano cewa kwamitin da ta kunshi Clement Ebri, Ahmed Mahmud Gumel, Chidi Duru, Clever Egbeji, Clever Ikisikpo da Jerry Ugokwe sun iso Legas a ranar Litinin inda suka shaidawa Ciyaman din APC na jihar, Tunde Balogun cewar suna bukatar ganawa da Ambode.

Balogun ya nuna kin amincewarsa ta ganawar saboda Ambode yana daya daga cikin 'yan takarar da za su fafata a zaben amma suka tursasa masa kuma ya kai su Alausa inda suka hadu da Ambode.

Bayan sun dauki hotuna tare da gwamna Ambode ya bukaci Balogun ya fice daga dakin domin yana son ganawar sirri da kwamitin zaben. Bayan misalin minituna 30 sai 'yan kwamitin suka fito suka ce za su koma wani Otal daban da Ambode ya tanadar musu.

Majiyar ta kara da cewa an hangi wasu na shiga da jakuna cikin dakunan Otel din da Ambode ya basu inda suka kasance a Otel din tare da wasu mukarraban Ambode guda biyu har wayewar gari yayinda sauran mutane ke zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel