Da duminsa: APC ta kori takarar tsohon IG Suleman Abba

Da duminsa: APC ta kori takarar tsohon IG Suleman Abba

Jam'iyyar APC mai mulki ta kori takarar kujerar Sanata da Suleman Abba, tsohon shugaban rundunar 'yan sanda ta kasa, ke yi a jiharsa ta haihuwa, Jigawa.

Sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ne ya sanar da haka yau, Talata, a Abuja.

Tsohon IG, Abba, na takarar neman kujerar sanata mai wakiltar jihar Jigawa ta tsakiya a karkashin jam'iyyar APC.

"Kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyyar APC bai amince da takarar Suleiman Abba na neman kujerar sanata a jihar Jigawa ta tsakiya ba," a cewar jawabin Nabena.

Da duminsa: APC ta kori takarar tsohon IG Suleman Abba, ta fadi dalili
Tsohon IG Suleman Abba
Asali: Twitter

Sannan ya kara da cewa, "sunan Suleman Abba da aka gani cikin 'yan takarar da aka tantance domin fafatawa a zaben fitar da dan takara, kuskure ne."

DUBA WANNAN: Waka a bakin mai ita: Tinubu ya bayyana dalilinsa na daina goyon bayan Ambode

Sai dai ya zuwa yanzu jam'iyyar ta APC ba ta bayyana dalilin soke takarar ta Barista Suleiman Abba ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel