Gwamnan Zamfara ya dakatar da zaben fitar da gwani na Jam’iyyar APC

Gwamnan Zamfara ya dakatar da zaben fitar da gwani na Jam’iyyar APC

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara ya dakatar da zaben fitar da gwani na takarar Gwamnan a karkashin Jam’iyyar APC a Jihar sa jiya saboda gudun rikici.

Gwamnan Zamfara ya dakatar da zaben fitar da gwani na Jam’iyyar APC
Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara ya dakatar da zaben APC
Asali: UGC

A lokacin da Abdulaziz Yari yake jawabi a Garin Gusau, yace babu ranar da za ayi zaben wanda Jam’iyyar APC za ta ba tikitin takarar Gwamna a zaben 2019 har sai ranar da aka bi sharudan da aka gindaya wajen tsaida ‘Dan takara..

Yari yace a matsayin sa na Gwamnan Zamfara kuma Jagoran Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar, ya dage zaben fitar da gwani kuma ba a sa Ranar da za a gudanar da zaben ba. Gwamnan yace kwamitin zaben ta sabawa abin da doka ta tsara.

KU KARANTA: Usani Usani zai nemi Gwamnan Jihar Kuros Riba a Jam'iyyar APC

Abdulaziz Yari yace a ka’ida, ‘Ya ‘yan Jam’iyya da kuma Shugabannin ta da Sakatarori ta ne kurum za su gudanar da zaben na tsaida’Yan takara. Sai dai kwamitin zabe na Jihar tayi watsi da wannan tsari da aka tanada inji Gwamnan Jihar.

Gwamnan wanda yace da su aka kafa APC kuma yana cikin manyan ta ba zai bari ayi abin da zai jawo rigima ba. Yanzu dai Allah kadai ya san Ranar da Jam’iyyar APC ta sa domin tsaida wanda zai yi mata takarar Gwamna a zabe na 2019.

Daga cikin masu neman Gwamnan Jihar akwai Ibrahim Wakala, Santa Kabir Garba Marafa, Mansur Dan-Ali, Honarabul Aminu Sani Jaji, Abu Magaji, Dauda Lawal da Mohammed Sagir Hamidu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel